logo

HAUSA

Emmanuel Macron: Za a janye sojojin Faransa daga Nijar kafin karshen bana

2023-09-25 10:25:44 CMG Hausa

Jiya Lahadi, shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya sanar da cewa, kafin karshen shekarar bana, za a janye sojojin kasarsa daga jamhuriyar Nijar.

Ya ce, kasar Faransa ta tura sojojinta ne zuwa kasar Nijar bisa gayyatar kasashen yankin, domin yaki da ta’addanci. Amma yanzu gwamnatin Nijar ba ta son ci gaba da yaki da ta’addanci, don haka, kasar Faransa za ta kawo karshen wannan hadin gwiwa na soja. Ya kara da cewa, za su tuntubi sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar game da janyewar sojojin kasar Faransa daga kasar, saboda kasarsa tana fatan aiwatar da aikin lami lafiya.

A sa’i daya kuma, Emmanuel Macron ya sanar da cewa, jakadan kasarsa dake Nijar, zai koma Faransa cikin sa’o’i masu zuwa. A baya dai gwamnatin mulkin sojan Nijar, ta bayar da umarnin korar jakadan kasar Faransa dake kasar.

Macron ya kuma ce, Faransa za ta ci gaba da hada kai da kasashen Afirka wajen yaki da ta’addanci, idan har zababbun gwamnatocin kasashen Afirka ko kungiyoyin shiyya-shiyya suka bukaci hakan. (Maryam)