Wannan dalili ya sa shawarar Ziri Daya da Hanya Daya samun karbuwa
2023-09-25 13:42:31 CGTN Hausa
Akon, shahararren mawaki dan asalin kasar Senegal, ya taba fadin cewa, “Turawa sun zo nahiyar Afirka wasu shekaru 400 da suka wuce, amma ba su yi komai ba, abun da ya sa har yanzu ake fama da koma bayan tattalin arziki a nahiyar Afirka. Yayin da a nata bangare, kasar Sin ta fara sa idonta kan nahiyar, nan take aka fara samun ingantattun hanyoyin mota, da sauran kayayyakin more rayuwa a kasashen Afirka.” Maganarsa ta nuna mana dalilin da ya sa kasar Sin, da shawararta ta “Ziri Daya da Hanya Daya” ke samun karbuwa a nahiyar Afirka, wato saboda suna haifar da hakikanin ci gaba a kasashe daban daban.
Kasar Sin ta gabatar da shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” wasu shekaru 10 da suka gabata, da zummar inganta aikin gina kayayyakin more rayuwa a kasashe daban daban, da tabbatar da hadewar masana’antunsu, don karfafa hadin gwiwar mabambantan kasashe, da ciyar da tattalin arzikinsu gaba.
Amma duk da haka, kasashen yamma sun yi ta kokarin shafa wa shawarar kashin kaji. Lokacin da kasar Sin take zuba karin jari a kasashen Afirka, sun ce wai “sabon nau’in mulkin mallaka” ne. Sa’an nan bayan da kasar Sin ta samar da bashi ga kasashen Afirka, su kasashen yamma sun ce wai “tarkon bashi” ne. Sai dai yawancin al’ummar kasashen Afirka suna da ra’ayi daya da na Akon, wato ba su yarda da zancen kasashen yamma ba. Domin sun gane wa idanunsu yadda kasar Sin ta kawo wa nahiyar Afirka abun da kasashen yamma suka ki samarwa.
Don tantance bambancin dake tsakanin hadin gwiwar da ake yi tare da kasashen yamma, da huldar hadin kai da kasar Sin, za mu iya duba misalin kasar Nijar.
Nijar kasa ce ta 5 mafi samar da ma’adinin Urainium a gida, sai dai wani kamfanin kasar Faransa mai suna Areva, shi ne ke mallakar ikon hakar duwatsun Urainium a kasar. Daga bisani, kamfanin ya yi kokarin magance biyan kudin haraji, ta yadda jama’ar kasar Nijar kusan ba za su samu wata moriya daga albarkatun Urainium din kasar su ba. Saboda haka, cikin shekaru 40 da suka wuce, kasar Nijar ta samar da kashi 25% na duwatsun Urainium da kungiyar tarayyar Turai (EU) ke bukata, da tabbatarwa kasar Faransa da kashi 30% na wutar lantarki da take samarwa a gida, yayin da ita kanta ke fama da tsananin talauci, inda kashi 12% na al’ummarta kawai ke da damar yin amfani da wutar lantarki.
To, a nasu bangare, mene ne ayyukan da kamfanonin kasar Sin suke yi a kasar Nijar? Suna kokarin baiwa kasar damar raya kanta. Wani kamfanin kasar Sin mai sarrafa danyen mai ya dauki nauyin gina ma’aikatun haka da sarrafa danyen mai a kasar Nijar, don taimakawa kasar kafa wani cikakken tsari na zamani ta fuskar sarrafa danyen mai, inda aka horar da ma’aikata ’yan janhuriyar Nijar dubu 105, gami da samar da karin guraben aikin yi kimanin 5000. Ban da wannan kuma, a halin yanzu, ana kokarin gina wani bututun mai da zai hada kasar Nijar da ta Benin, inda ake sa ran ganin bututun ya samar da gudunmowa ga ci gaban tattalin arzikin kasashen 2.
Sai dai ina dalilin da ya sa kasar Sin, da shawararta ta “Ziri Daya da Hanya Daya” ke iya haifar da hakikanin ci gaba a kasashen Afirka da sauran kasashe masu tasowa?
Wani dalili shi ne wata ka’idar da ake bi wajen aiwatar da shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya”, wato “A tattauna tare, da gudanar da aiki tare, gami da more sakamakon da aka samu tare”. Inda kasar Sin ta kan tattauna tare da kasar da take hadin gwiwa da ita, don tabbatar da ganin kasancewar duk wani aiki, da jarin da ake zubawa, da tsarin hadin kan masana’antu, abu ne da abokiyar hulda ke bukata. Kana za a yi kokarin daidaita matsalar da ke hana ruwa gudu, don tabbatar da ci gaban tattalin arzikinta. Bisa wannan ka’ida ne, aka gina layin dogo na Mombasa-Nairobi, don hada tashar jirgin ruwa ta Mombasa irinta mafi girma a gabashin Afirka, da sauran kasashen dake tsakiyar nahiyar Afirka, ta yadda karin kasashe za su samu damar fitar da kayayyakinsu zuwa ketare ta jiragen ruwa; kana a nahiyar Asiya, layin dogo na Jakarta-Bandung ya haifar da damar samun karuwar tattalin arziki ga daukacin kasashen dake kudu masu gabashin Asiya…
Ban da haka, wani dalili na tushe da ya sa kasar Sin ke iya taimakawa sauran kasashe samun ci gaban tattalin arziki, shi ne tsarin siyasa na kasar. Mun san kasar Sin kasa ce mai bin tsarin siyasa na Gurguzu. Wannan halayya ta sa ta kokarin neman samun wadatar bai daya a tsakanin al’ummarta, da gina “al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makoma ta bai daya” a duniya. A sa’i daya kuma, wannan tsarin siyasa ya sa kamfanonin kasar ke zama karkashin kulawar gwamnati, da kokarin bin manufofin kasar, ta yadda ake samun damar aiwatar da wasu nagartattun matakai masu adalci da hangen nesa, irinsu “kokarin amfanar da juna”, da taimakawa sauran kasashe don su samu kwarewar raya kansu. (Bello Wang)