Ga Dukkan Alamu Japan Ta Zama Butulu
2023-09-25 15:43:32 CMG Hausa
Zubar da ruwan dagwalon nulikiyar Japan a cikin teku na ci gaba da ɗaukar hankali a duniya yayin da shugabannin ƙasashe makwabta tekun Pacifik suka ci gaba da nuna adawarsu a bayyane a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 78.
Firaministan Tsibirin Solomon Manasseh Sogavare, a yayin da yake gabatar da jawabinsa a babban zauren muhawarar majalisar, ya caccaki ƙasar Japan, da rahoton tantancewa na Hukumar Makamashin Nukiliya (IAEA) ta Duniya game da rashin nuna gaskiya da cin zarafin ƙasashe mazauna yankin Pasifik.
Bari mu dan waiwayi baya kaɗan, tarihi ya nuna cewa, shekaru goma sha biyu da suka gabata, bayan haɗarin nukiliyar Fukushima, Japan ta samu taimako daga sassa daban-daban a faɗin duniya. Bayan wadannan shekarun 12, Japan ta yanke shawarar sanya dukkan bil'adama cikin haɗarin gurɓacewar nukiliyarta. Alhalin Yarjejeniya ta shekarar 1972 kan rigakafin gurɓacewar ruwa ta hanyar zubar da sharar gida da sauran al'amura ta hana gurɓata teku, da kuma yarjejeniyar Majalisar Ɗinkin Duniya kan dokar teku ta tanadi cewa ƙasashe na da alhakin kare da kiyaye muhallin ruwa.
Gwamnatin Japan ta fara zubar da ruwan dagwalon nukiliya sama da tan miliyan guda a cikin teku. Mutane da dama sun fusata da wannan yunƙuri, ciki har da gwamnatoci da dama, waɗanda a hankali suna ganin wannan zaɓi a matsayin cin amanar al’umma da wulakanta amincin duniya.
Baya ga yin watsi da bayanan kimiyya, shawarar ta kuma keta dokar ruwa ta ƙasa da ƙasa da kuma 'yancin ɗan Adam na mutanen Japan da Pacifik, musamman ma damuwar masunta.
Duk da damuwar al'ummar cikin gida da na ƙasa da ƙasa, Japan ta dage kan yin amfani da tekun Pasifik a matsayin "wurin zuba shararta" ta hanyar zubar da ruwan dagwalon nukiliya a cikin tekun.
A daidai wannan gaɓar sai mu gabatar da wasu tambayoyi masu muhimmanci. Shin na’urorin tsarkake ko tsaftace tekun na Japan zasu ci gaba da yin aiki da kyau cikin shekaru talatin masu zuwa? A lokacin da ruwan dagwalon da ta zuba cikin tekun ta wuce iyakar mizani? Shin za a iya sanar da al'ummar duniya cikin gaggawa? Menene illar da wannan gubar zata yi wa teku na dogon lokaci akan tsaro da abinci, da lafiyar ɗan Adam, da yanayin ruwa? Rahoton Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) bai bayar da amsar wadannan tambayoyi ba.
Bugu da ƙari, gwamnatin ƙasar Japan na da niyyar sake kunna wutar lantarki da ƙarin makamashin nukiliya duk da alamun girgizar ƙasa da hatsarin tsaro, da bala'in nukiliyar da ke gudana, da kuma ɗimbin kuɗaɗen jama'a da ake buƙata. Bayan sanin cewa halin gaggawar da yanayin duniya ke ciki na buƙatar amintattun hanyoyin samar da makamashi mai tsafta, kamar iska da hasken rana, wadanda dabarun makamashi na gwamnatin ƙasar na yanzu ba za su iya samarwa ba.
A matsayin muhimmiyar hanyar kasuwancin duniya, Tekun Pasifik gida ne ga dukkan ƙasashen yankin. Dan Adam na iya fama da gurɓacewar tekun Pasifik, tare da sakamako mai illa. Kafin Japan ta yi wannan mummunar yunƙurin, an yi fatan hukumar ta IAEA za ta ɗauki ƙarin lokaci tare da zurfafa bincike, da yin la'akari da dukkan abubuwan da za su iya haifar da haɗari.
Dole ne dukkan gwamnatoci da ƙasashe da ke da alhakin sake tantance tasirin wannan mummunar shawarar ga bil'adama su farga. Kira anan ita ce a gudanar da bincike na biyu a cikin hanyar da ta dace kuma a kai ga yanke shawara mafi aminci ga bil'adama. (Yahaya)