logo

HAUSA

Somaliya da ATMIS sun yi tir da harin bam da aka kai tsakiyar Somaliya

2023-09-25 10:05:55 CMG HAUSA


Mahukuntan Somaliya da tawagar wanzar da zaman lafiya ta kungiyar Tarayyar Afirka ko ATMIS a takaice, sun yi Allah wadai da harin kunar bakin wake da 'yan ta'addar Al-Shabab suka kai a birnin Beledweyne dake tsakiyar kasar Somaliya, harin da ya haddasa mutuwar mutane a kalla 20 tare da jikkata wasu da dama.

A sanarwar da shugaban kasar Somaliya, Hassan Sheikh Mohamud, da Mohammed El-Amine Souef, wakilin musamman na shugaban hukumar gudanarwar AU a Somaliya, kana shugaban ATMIS suka fitar daban-daban, sun lashi takwabin kara kaimi wajen tabbatar da zaman lafiya a Somaliya, duk da karuwar hare-haren da kungiyar ta'addanci take kaddamarwa.
Haka kuma, shugaba Mohamud ya aike da sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda suka mutu tare da yi wa wadanda suka jikkata fatan samun sauki.
Wani dan kunar bakin wake ne dai ya tayar da nakiya a cikin wata babbar mota makare da bama-bamai a wani shingen binciken jami'an tsaro dake kusa da wata kasuwa da gidajen mai guda biyu a birnin Beledweyne dake yankin Hiran.
Rahotanni na cewa, an garzaya da wasu daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su ta jirgin sama zuwa Mogadishu, babban birnin Somaliya, domin samun kulawa ta musamman.
A nasa bangare, Mohammed El-Amine Souef ya ce, harin da aka kai kan fararen hula da ba su ji ba su gani ba, an yi shi ne da nufin karkatar da hankalin jama’a dangane da gagarumin asarar da kungiyar al-Shabab ta tabka a hare-haren da gwamnati ke ci gaba da kaiwa da nufin murkushe su. (Ibrahim Yaya)