logo

HAUSA

Me ya haifar da ambaliya a Libya?

2023-09-25 22:29:08 CMG

Daga Lubabatu Lei

A jiya ne agajin jin kai da gwamnatin kasar Sin ta samar ya isa Libya.

Bisa alkaluman da hukumar Libya ta samar a ranar 23 ga wata, an ce, mutanen da ambaliyar ta halaka wadanda aka yi rajistarsu tuni adadinsu ya kai 3845. Sai dai sakamakon yadda dubban mutanen da suka bace, yawan mutanen da ambaliyar ta halaka a hakika zai zarce wanann adadin da yawan gaske. Munanan illolin da ambaliyar ta haifar sun kuma sa mutane sun fara tunani game da me ya haifar da wannan mummunar masifa?Wasu sun ce bala’i ne daga indallahi, amma karin mutane na ganin cewa, Amurka da sauran kasashen yamma ne ya kamata su dauki nauyinta.

Birnin Derna da ke gabashin kasar Libya shi ya fi fuskantar barnar da ambaliyar ke haifarwa, inda ambaliyar ta rushe wasu madatsan ruwa biyu na wurin, lamarin da ya sa ambaliyar ta lalata unguwannin birnin da dama.An ce, madatsan ruwa da suka rushe a sanadin wannan ambaliya tuni suka fara yoyo, kuma mai aikin gudanar da madatsan ruwan da kuma masana suka yi gargadin hadarin da ake iya fuskanta. A lokacin mulkin Muammar Gaddafi, gwamnatin Libya ta taba cimma wata yarjejeniya tare da wani kamfanin kasar Turkiyya game da gyara madatsan ruwan, amma sakamakon yadda Amurka da sauran kasashen yamma suka hambarar da shugaban na Libya a shekarar 2011 da sunan wai kare fararen hula daga mulkin Gaddafi, tuni yarjejeniyar ta zama a banza. Daga nan kuma, Libya ta tsunduma cikin yakin basasa da baraka, lamarin da ya sa aka dakushe karfin kasar, manyan ababen more rayuwa na kasar ma sun lalace, abin da kuma ya rage karfin kasar wajen rigakafin bala’u da ma tinkararsu. Da a ce tsarin hasashen bala’u na kasar na gudana yadda ya kamata, kuma an gyara madatsan ruwan cikin lokaci, da an kai ga magance mutuwar akasarin mutanen a ambaliyar.

Libya kasa ce da ke da mafi yawan man fetur da aka gano a nahiyar Afirka, wadda ya kamata al’ummarta suka ji dadin rayuwar wadata, amma ga yanayin da suka samu kansu a ciki. Ma iya ce, Amurka da sauran kasashen yamma ne suka jefa su a cikin wannan mawuyacin hali. Kamar yadda wasu masu bibiyar shafukan sada zumunta suka ce, “Yadda kasashen yamma suka kaddamar da yaki a Libya da ma kakaba mata takunkumi bayan yakin, sun sa wa kasar tarnaki wajen tabbatar da ci gabanta, abin da ya sa kasar da a baya ta kasance tamkar aljanna ta tsumdumma cikin wuta.” “Ambaliyar da ta afkawa Derna ba safai a kan ga irinta ba a tarihi, duk da haka, kasashen yamma ne suka haifar wa al’ummar Libya wannan mummunar masifa sakamakon yadda suka kutsa cikin kasar.” (Mai Zane:Mustapha Bulama)