logo

HAUSA

Ministan Masar: Bankin AIIB na taka muhimmiyar rawa wajen samun ci gaba mai dorewa a Afirka

2023-09-25 09:57:56 CMG HAUSA

Ministan harkokin kudi na kasar Masar Mohamed Maait ya yaba da muhimmiyar rawa da bankin zuba jari kan kayayyakin more rayuwa na Asiya (AIIB) ya taka, wajen samar da bunkasuwa mai dorewa a nahiyar Afirka.
Maait ya bayyana haka ne a gabar da ake shirye-shiryen bude taron shekara-shekara na mambabobin hukumar gudanarwar bankin AIIB karo na 8, wanda aka shirya gudanarwa daga yau Litinin zuwa gobe Talata 26 ga watan Satumban da muke ciki.
Taron na shekarar 2023 mai taken "Ci gaba mai dorewa a duniya mai fama da kalubale”, wani muhimmin al'amari ne ga hukumar gudanarwar bankin AIIB, yayin da yake nuna dawowar bankin na gudanar da taronsu a zahiri, wanda rabon hakan, tun shekarar 2019, kana taronsa na shekara-shekara na farko a nahiyar Afirka.
Ministan ya ce, Masar a matsayinta na kasar dake karbar bakuncin taron, za ta kasance "muryar Afirka" a taron. Yana mai jaddada aniyar kasar, ta taka rawar gani a harkokin da suka shafi Afirka.
Ya jaddada bukatar bankin da ya kara ware wasu kudade, don saka jari a wasu muhimman sassa kamar sufuri, da sadarwa, da makamashi don ci gaban nahiyar Afirka. (Ibrahim Yaya)