logo

HAUSA

Amurka: ‘yan makarantar sakandare suna fama da matsalar tunani

2023-09-24 02:00:14 CMG Hausa

 

Cibiyar dakile da kandagarkin cututtuka ta kasar Amurka wato CDC a takaice, ta kaddamar da sakamakon binciken dake cewa, ‘yan makarantar sakandare suna fama da matsalar tunani a Amurka, wanda ya wuce zaton mutane kwarai da gaske, musamman ma ‘yan mata, inda kusan kaso 60 na ‘yan mata ke fama da yanayin bakin ciki, ko kuma rashin fatan alheri.

Kamfanin dillancin labaru na “The Associated Press” ya ruwaito cewa, a lokacin kaka na shekarar 2021 ne cibiyar CDC ta gayyaci ‘yan makarantar sakandare fiye da dubu 17, su amsa tambayoyi cikin takarda. Masu nazari daga cibiyar sun gano cewa, a cikin watanni 12 da suka wuce, ‘yan makarantar da yawansu ya wuce kaso 40 ne suka taba fama da bakin ciki, ko rashin fatan alheri a kusan ko wace rana cikin makonni 2 a jere, har ta kai ba su iya zaman rayuwa yadda ya kamata ba. Adadin ya kai kaso 57 cikin ‘yan mata, da kuma kaso 29 cikin maza.

A shekarar 2011 kuma, adadin ya kai kaso 36 cikin ‘yan mata, da kuma kaso 21 cikin maza. Haka kuma, wasu ‘yan makarantar sakandare da yawansu ya kai kaso 22, sun taba yin tunanin kashe kansu. Adadin ya kai kaso 30 cikin ‘yan mata, wanda ya fi na maza yawa har sau biyu, kuma ya karu da kaso 60 bisa na shekarar 2011.

A cikin binciken da aka gudanar, ‘yan mata da yawansu ya kai kusan kaso 20 ne aka ci zarafinsu ta hanyar lalata, a watanni 12 da suka wuce, yayin da wasu da yawansu ya kai kashi 1 cikin kashi 7 aka tilasta musu yin jima'i.

Debra Houry, babbar jami’ar kula da aikin jinya a cibiyar CDC ta yi karin bayani da cewa, wadannan alkaluma suna sanya mutane damuwa sosai. Karin ‘yan mata Amurkawa suna shiga yanayi na bakin ciki, saboda ana cin zarafinsu, tare da ji musu rauni.

Mitch Prinstein, babban jami’in kula da aikin kimiyya, a hadaddiyar kungiyar masu aikin ilmin tunani ta Amurka yana ganin cewa, kamata ya yi a dauki matakai don kyautata lafiyar tunanin matasa Amurkawa. Ya dace a koyar da su yadda za su daidaita matsin lamba, da rikici ta hanyar da ta dace, kamar yadda ake koyar da su kiwon lafiyar jiki ta hanyar motsa jiki.

Madam Debra Houry tana ganin cewa, makaranta na taka muhimmiyar rawa wajen kiyaye lafiyar tunanin ‘yan makaranta. Kamata ya yi a inganta horas da ma’aikatan makaranta da malamai, don su gano matsalolin tunani da ‘yan makaranta suke fuskanta kan lokaci, da kuma taimaka musu daidaita su.

Dangane da lamarin, madam Zhang Chuji, likita da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing, tana da wata shawara, ta jaddada muhimmancin tuntubar matashi, inda ta ce, wajibi ne iyaye su kara yin ma’amala da ‘ya’yansu kullum, su yi kokarin fahimtar ‘ya’yansu. (Tasallah Yuan)