logo

HAUSA

Mutane 35 ne suka mutu a wata gobarar da ta tashi a rumbun ajiyar man fetur a Benin

2023-09-24 17:05:26 CMG

Ma’aikatar harkokin cikin gidan da tsaron jama’a ta kasar Benin ta sanar cewa, akalla mutane 35 ne suka mutu, yayin da wasu fiye da goma suka samu munanan raunuka sakamakon wata gobara da ta tashi a wani wurin ajiyar man fetur a ranar Asabar da ta gabata, a yankin Oueme dake yankin kudu maso gabashin kasar Benin.

Wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar ta ce gobarar ta tashi ne a wani gari da ke kusa da kan iyaka da Najeriya, a lokacin da ake sauke jarkunan man fetur daga mota da misalin karfe 9:30 na safe agogon wurin.

Nan take jami’an hukumar kashe gobara da ‘yan sanda da kuma tawagogin likitoci suka hada kai domin shawo kan lamarin, in ji sanarwar, inda ta kara da cewa ofishin mai shigar da kara na gwamnati ya bude cikakken bincike kan musabbabin hatsarin. (Yahaya)