logo

HAUSA

Firaministan Tsibiran Solomon: Zubar da ruwan dagwalon nukiliyar Japan cikin teku hari ne ga amincin duniya

2023-09-24 16:59:19 CMG

A ranar Juma’ar da ta gabata ne firaministan tsibiran Solomon Manasseh Sogavare ya yi Allah wadai da zubar da ruwan dagwalon nulikiyar Japan a cikin teku, ya bayyana hakan a matsayin wani hari kan amana da hadin kan duniya.

Tsibiran Solomon na goyon bayan mazauna tsibirin Pacific masu ra'ayi iri daya, kuma sun yi matukar kaduwa da shawarar da Japan ta yanke na zubar da sama da tan miliyan 1 na ruwan dagwalon nukiliya cikin teku, a cewar Sogavare a babban taron Majalisar Dinkin Duniya.

"Rahoton tantancewa na Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya ba ta cika ba, kuma bayanan kimiyyar da aka fitar ba su wadatar ba, kuma suna cike da son zuciya, yayin da aka yi watsi da wadannan damuwar," a cewar sa.

Firamininstan ya ci gaba da cewa, Idan ruwan dagwalon nukiliyar ba ta da hadari, kamata ya yi Japan ta adana ruwan a kasarta, kasancewar an zubar da ruwan dagwalon a cikin teku na nuni da cewa tana da hadari.

"Muna kira ga kasar Japan da ta binciko wasu hanyoyin da za a bi wajen tunkarar batun ruwan dagwalon nukiliyar da ta ce ta tsaftace, sannan ta daina zubar da ruwan a cikin tekun Pacific."  "Idan har za mu sake kyautata aminci da kuma farfado da hadin kan duniya, dole ne mu kasance masu gaskiya wajen kare tekunan mu wanda shi ne jigon rayuwar al'ummarmu." (Yahaya)