logo

HAUSA

Dagwalon Nukiliyar Japan: Kar Duniya Ta Rungume Hannu Kilu Ta Ja Bau

2023-09-24 21:25:21 CGTN Hausa

Daga Abdulrazaq Yahuza

A yau ne ake cika wata guda da fara zubar da dagwalon tashar Nukiliyar Fukushima ta Japan a cikin Tekun Pacific, lamarin da ya haifar da tir da Allah-wadai da kuma fargabar illar da abin zai yi ga rayuwar bil’adama a doron kasa da kuma halittun da ke cikin ruwa.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne firaministan tsibiran Solomon Manasseh Sogavare ya yi Allah wadai da zubar da ruwan dagwalon nulikiyar Japan a cikin teku, ya bayyana hakan a matsayin wani hari kan amana da hadin kan duniya. "Rahoton tantancewa na Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya ba ta cika ba, kuma bayanan kimiyyar da aka fitar ba su wadatar ba, kuma suna cike da son zuciya, yayin da aka yi watsi da wadannan damuwar," a cewar sa. Firamininstan ya ci gaba da cewa, Idan ruwan dagwalon nukiliyar ba ta da hadari, kamata ya yi Japan ta adana ruwan a kasarta, kasancewar an zubar da ruwan dagwalon a cikin teku na nuni da cewa tana da hadari.

Dagwalon da Japan ke zubarwa da adadinsa ya haura sama da tan miliyan daya daga ranar 24 ga Agustan 2023, ana iya shafe kimanin shekara 30 ana yi ba a kammala ba.

Adawa da abin da Japan ke yi daga masu ruwa da tsaki kan sha’anin teku ya tabbatar da kin amincewa da ikirarin gwamnatin kasar na cewa an tsaftace dagawalon. Daga cikin gida, wani gungun mazauna kasar a karkashin Majalisar Hulda da Jama'a ta kasa da ke adawa da zubar da dagwalon masana'antun makamashin nukiliya, sun shigar da kara a ofishin Gundumar Tokyo. Inda suka zargi Firayim Minista Fumio Kishida da Shugaban Kamfanin Lantarki na Tokyo (TEPCO) Mista Tomoaki da nuna sakaci kan wannan al’amari.

Masu koken sun bayyana cewa dagwalon na dauke da makamashi mai guba baya ga sinadarai masu hadari da ke narkewa wanda ba zai yiwu a raba shi da dagwalon ba ko da bayan an tsaftace shi. Suka kara da cewa har yanzu wannan babbar barazana ce ga kiwon lafiyar dimbin mutanen da suke cin naman dabbobin ruwa.

Har ila yau, akwai masana kimiyya da suka nuna shakku game da rashin hadarin dagwalon da Japan ke zubarwa. A rahoton da Kungiyar Masu Zurfafa Binciken Kimiyya ta Amurka da ke Birnin Washington, ta wallafa a 2021, ta ce akwai yiwuwar a samu wasu sinadaran makamashi masu guba da ke daukar tsawon lokaci ba su narke ba, da za su iya silalewa yayin gudanar da aikin tsaftace dagwalon.

Bugu da kari, a mukalar da ya rubuta, mai taken "Shin dagwalon Fukushima ba shi da hadari? Abin da kimiyya ta ce" da aka buga a Mujallar “Nature” cikin watan Yuni, masanin halittun ruwa, Mista Robert Richmond daga Jami'ar Hawaii ya yi tambaya: "Shin mutanen da ke sahihantar da wannan (fitar da dagwalon makamashin nukiliya na Japan)… sun nuna gamsuwarmu ne cewa zai kasance ba tare da wani hadari ba ga lafiyar Dan’adam da kuma teku? "Amsar ita ce a'a," in ji Richmond.

Shi ma daya daga cikin masana kimiyya biyar na kwamitin ba da shawara ga Dandalin Tsibiran Pasifik, Richmond ya ce bayan nazarin bayanai daga Kamfanin Lantarki na TEPCO da Gwamnatin Japan, da kuma ziyartar tashar nukiliyar Fukushima, ba a magance zargin da ke cikin fitar da dagwalon ba.

Bisa bayanan masanan, zubar da dagwalon a teku zai haifar da mummunar illa ga muhalli da za a dade ba a magance ba, sakamakon makamashi da sinadarai masu hadari ga halittun ruwa da ‘yan adam musamman masunta da mutanen garuruwan da ke gabar teku.

Bayanai na nuna cewa damuwar da aka shiga kan zubar da dagwalon ta jefa shakku a zukatan mutane musamman wadanda ke zama a kusa da tashar Fukushima game da abin da gwamnatin Japan ke yi, sakamakon har yanzu ba su manta da yadda aka yi tafiyar hawainiya wajen sanar da su bayanan da suka kamata ba bayan ibtila’in da ya auku a 2011.

Masu kare hakkin Dan adam na Majalisar Dinkin Duniya su ma sun nuna adawa da abin da Japan ke yi, haka su ma masu rajin kare lafiyar muhalli. Kungiyar Kare Lafiyar Muhalli ta Greenpeace ta fitar da rahotannin da suka nuna shakku a kan matakan da Kamfanin TEPCO ke amfani da su wajen tsaftace dagwalon, inda ta yi zargin cewa ba a zurfafawa ta yadda za a magance illar da abin ka iya haifarwa.

Ita ma Kasar Sin ta nuna rashin jin dadinta da zubar da dagwalon na Japan a teku. Rahotanni sun nuna cewa tuni kasar ta dauki matakin rage yawan abincin da ake samu daga teku da kasar ke sayowa daga Japan.  A kasar Koriya ta Kudu ma, wani sauraron ra’ayoyin jama’a da aka gabatar kwanan baya, ya nuna kashi 80 cikin 100 na mutanen kasar sun nuna damuwa kan fitar da dagwalon.

Wasu na iya tunanin cewa, watakila Japan ba ta da zabi ne illa ta antaya dagwalon a teku, sai dai kuma ba haka ba ne. Wani babban masanin kimiyya a Cibiyar Binciken Kimiyyar Teku da Muhalli ta Woods Hole Oceanographic da ke Birnin Massachusetts na Amurka, Mista Ken Buesseler, ya ce kamata ya yi Japan ta zubar da dagwalon a kan-tudu, “domin zai fi saukin sa ido da kula da abubuwan da ka iya haifarwa.” Haka nan da an hada da zabin gauraya dagwalon da kankare wajen fitarwa.

Matukar kasashen duniya suka rungume hannu suka bari wannan dabi’a ta Japan ta ci gaba, tabbas kilu za ta jawo bau, domin kamar yadda Mista Buesseler ya nuna fargaba a kai, abin da Japan ke yi na iya bude kofa ga wasu kasashe ta zubar da dagwalon nukiliyarsu a teku. Riga-kafi dai ya fi magani!