logo

HAUSA

Kungiyoyin kasa da kasa na ci gaba da tallafawa Gwamnatin jihar sokoto wajen ayyukan raya kasa

2023-09-24 15:46:24 CMG Hausa

Gwamnan jihar Sokoto Alhaji Ahmed Aliyu ya tabbatar da cewa kaso 60 na adadin ayyukan cigaba da ya gudanar a jihar, an yi su bisa tallafin kungiyoyin agajin kasa da kasa.

Gwamnan ya na magana ne lokacin da yake karbar bakuncin wakilan gidauniyar Türkiye Diyanet dake bayar da agaji ga mabukatan kasashe, lokacin da suka ziyarci jihar domin kaddamar da wasu ayyukan samar da ruwa da tallafawa marayu.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

 

Gwamnan na jihar ta Sokoto a don haka ya bukaci gidauniyar ta Türkiye Diyanet da ta kara fadada ayyukan ta a jihar musamman a fagen sha`anin samar da ruwan sha da karatun kananan yara kasancewar jihar Sokoto na daya daga cikin jahohin dake arewacin Najeriya da suke da yawan marayu da ba sa iya zuwa makaranta sakamkon matsalolin hare-haren `yan ta`adda.

Ya cigaba da cewa gwamnatin jihar ta Sokoto zata kara himmatuwa sosai wajen yin hadaka da kasashen duniya wajen sake gina jihar, yace kudaden da ya yi aiki da su a tsawon watannin da ya yi akan mulki ba kudi ba ne da ya samu daga gwamnatin tarayya ba ko kuma kudin gwamnatin jihar, kudade ne na tallafi daga kasashen duniya.

“Mu kan mika hannayen mu zuwa ga kasashen duniya da suka cigaba domin neman tallafi a shigo a taimaka mana, wannan foundation Türkiye Diyanet da ta fito daga kasar Turkiyya ya dade yana taimakawa mutane a fadin duniya, inda ya taimakawa kasashe 149 kuma Allah ya sa jihar Sokoto ta shigo daga cikin jahohin da suka amfana daga ayyukan ta, kuma bisa tattaunawar da muka yi da su sun yi alkawarin za su taimakawa mutane marasa galihu ta hanyar taimakawa marayu, ta hanyar bayar da ruwan sha da kuma ta hanyar daukar nauyin karatun `yan asalin jihar domin su je Turkiyya su karo karatu”

A lokaci da yake jawabi, Malam Muhammad Abdulwahab babban jami`in gidauniyar a arewacin Najeriya ya ce sun fara aiki a jihar Sokoto ne tun a watan disambar shekarar bara inda suka gina rijiyoyin burtsatsai a kauyuka da dama da suke fama da matsanancin rashin ruwa kari akan sauran ayyukan jin kai da suke tallafawa masu rauni musamman mata da kananan yara dake jihar ta Sokoto.(Garba Abdullahi Bagwai)