logo

HAUSA

Wasannin da ake yi a waje na samun karin karbuwa a kudu maso yammacin Sin

2023-09-22 20:43:54 CRI

Lardin Guizhou na kudu maso yammacin Sin, wanda a baya ake yiwa lakabi da “Yankin Kwazazzabai" saboda sarkakiyar sa, da tsaunuka masu tsayi, a yanzu ya sauya yanayi zuwa wurin gudanar da wasannin kasada, da sauran wasanni da ake yin su a waje.

Frederic Moal, wanda ya shafe shekaru 8 yana rayuwa a kasar Sin, na cikin masu sha’awar wasannin kasada. Kuma ya samu sha’awar irin wadannan wasanni ne daga mahaifin sa, inda Frederic ya fara koyon wasan tseren babura cikin turbaya, wanda ake yiwa lakabi da “BMX” tun yana karami sosai, ya kuma yi ta kokarin zama kwararren mai gudanar da wannan wasa na BMX.

A shekarar 1982, bayan ya samu kwarewa sosai, Moal ya kafa kungiyar masu wasan BMX a Faransa, inda ya kasance mai horas da ‘yan wasa. Saboda kwarewar da ya samu, ya kai ga lashe lambar karramawa a gasar BMX ta turai, wadda aka gudanar a Faransa a shekarar 2009.

A watan Maris din bana, Moal ya amince ya zama babban koci na kungiyar wasan BMX dake Guizhou. A cewar sa "Wannan ne karon farko da nake aikin horaswa a Sin, kuma tabbas aiki ne mai cike da kalubale, amma duk da haka mambobin kungiyar mu a shirye suke, kuma suna da kwarin gwiwa. Ko da yake mun fara ne tun daga tushe, ina da imanin cewa kungiyar BMX ta Guizhou za ta ginu, har ta kai matsayin koli".

Game da dalilan sa na zama a Sin, domin aikin horas da ‘yan wasan BMX kuwa, Moal ya ce Guizhou yanki ne mai tsaunuka na yawon bude ido, kuma wurin yana da albarkatun wuraren wasanni. Ya ce "Ina matukar son wannan wuri. A gani na wurin zai wanzar da wasannin da ake yin su a tsaunuka. Dorewar hakan na da matukar muhimmanci wajen kare tsaunukan da ma daji. Ina fatan zan bayar da babbar gudummawa ta raya wasannin tseren babura da ake yi a tsaunukan dake Guizhou. Kana ina fatan za mu yi nasarar lashe gasanni na gida da na ketare".

A daya bangaren kuwa, Jan Beranek, dan asalin kasar Czech, kuma kwararre a wasannin kasada, da maye gurbin taurarin fina-finai wajen aiwatar da kasada, ya gina sana’ar sa a Guizhou.

Duk da cewa Jan Beranek yana aiki a matsayin injiniyan fasahohin sadarwa, a hannu guda kuma, mai horas da ‘yan wasan saukar lema ne. Ya zuwa yanzu, ya yi saukar lema sama da sau 1,000, yana kuma cike da nishadin gudanar da saukar lema a Guizhou.

Jan Beranek ya ce "Dama ce mai daraja na samu ta yin saukar lema daga gadar Beipanjiang dake Guizhou, wadda ita ce gada mafi tsayi a duniya. Yanayin hangen kasa, da tsaunuka, da ita kan ta gadar na da matukar ban sha’awa. Gadar na da matukar tsayi, kuma sauka zuwa kasan ta na da nisan gaske. Don haka muna da isasshen lokaci na sarrafa jiki, da alkafira kafin kaiwa kasa. Kaza lika akwai isasshen lokaci na na yin shawagi a sama kafin kaiwa kasa lami lafiya"

Kasancewar yankin a sashen tuddan Yunnan-Guizhou yana kudu maso yammacin kasar Sin, mai cike da kwazazzabai, Guizhou ya taba kasancewa wuri mai cike da duwatsun hamada. Ta yadda yawan tsaunukan sa suka hana shi samun ci gaba, tare da dakile dunkulewarsa da sauran sassan duniya.

To sai dai kuma, a gwamman shekarun baya bayan nan, an gina gadojin zamani a Guizhou. Wadannan ababen more rayuwa sun samar da zarafi na zirga zirgar jiragen kasa masu saurin tafiya, wadanda ke hade wurare masu nisa, ta yadda ake iya gudanar da wasannin da ake yi a waje cikin sauki a yankin.

A yau, yankin kwazazzabai na Guizhou, ya fita daga kangin rashin ci gaba. Maimakon haka, yana ta kara zama wurin gudanar da wasanni da ake yi a waje, ciki har da tseren babura cikin tsaunuka, da gudun yada kanin wani, da hawa duwatsu, da tafiya kan kogi, da shiga kogo, da wasan taka igiya domin tsallake manyan tsaunuka, da saukar lema daga manyan tsaunuka.