logo

HAUSA

Sakatare Janar na MDD ya yi kira da a yi kokarin samar da zaman lafiya a duniya

2023-09-22 10:29:22 CMG Hausa

Sakatare janar na MDD Antonio Guterres ya yi kira da a yi kokarin samar da zaman lafiya ga kowa. Antonio Guterres ya yi kiran ne a jiya Alhamis, albarkacin ranar Zaman Lafiya ta Duniya.

Sakatare janar din ya jaddada cewa, samun zaman lafiya ya dogara ne da sakamakon matakin da aka dauka, matakin da zai gaggauta kai wa ga samun nasarar cimma muradun ci gaba masu dorewa da tabbatar da babu wanda aka bari a baya.

Haka kuma, mataki ne na kawo karshen yaki da tasirinsa a duniya, da daukakawa da kare mutunci da hakkokin bil adama da amfani da diflomasiyya da tattaunawa da hadin gwiwa wajen yayyafawa tashe-tashen hankula ruwan sanyi da kawo karshen rikice-rikice da daukar matakin taimakawa miliyoyin mutanen dake rayuwa cikin radadin yaki.

Ana gudanar da ranar Zaman Lafiya ta Duniya ne a ranar 21 ga watan Satumban kowacce shekara. Babban zauren MDD ne ya ayyana wannan rana domin karfafa akidun zaman lafiya ta hanyar daukar sa’o’i 24 na kauracewa rikice-rikice da dakatar da bude wuta. (Fa’iza Mustapha)