logo

HAUSA

Manoman shinkafa a jihar Kebbi sun bayyana fargabar fuskantar fari a bana

2023-09-22 14:07:52 CMG Hausa

Manoman shinkafa a jihar Kebbi dake arewacin Najeriya sun bayyana fargabar fuskantar asara mai yawa a bana sakamakon matsalar karancin ruwa.

A lokacin da suke zantawa da manema labarai a birnin Kebbi, wasu daga cikin masu noman shinkafar sun ce idan har hukumar kula da kogunan Rima ba ta sako ruwa ba daga madatsar ruwan Goronyo, tabbas shinkafar da suka shuka a kan tudu ba za ta nuna ba har zuwa girbi.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Manoman dai sun bayyana cewa sakamako karancin ruwan sama da aka fuskanta a damunar bana a jihar, akwai bukatar mahukunta sun bude madatsar ruwan Goronyo wanda zai taimakawa shinkafa ta samu nuna.

“Muna kira ga gwamnatin jiha don Allah ta sanya mana hannu a samar mana da ruwa, a bude dam saboda jama’a su wadata da amfanin gonakinsu, in har ba a bude dam ba aka gaza samun shinkafar damuna, to babu tabbacin a iya noman shinkafa da rani.”

“Muna neman taimako don Allah da gwamnatin jiha da ta tarayya da duk wanda yake da hannun game da wannan al’amari don Allah ya taimaka mana da ruwa a sako mana shi tun da dai akwai shi.”

A lokacin da take bayani game da koke-koken manoman, babbar jami’a mai lura da hukumar kogunan Rima a jihar Kebbi Injiniya Mariyatu Sulaiman ta alakanta rashin ruwan ga matsalar sauyin yanayi a duniya baki daya.

Amma duk haka ta ce, ta samu zantawa da manajan madatsar ruwa ta Goronyo kuma ya ba ta bayanin cewa, “Labarin da na samu shi ne a bana hakika ba a samu ruwan damuna da yawa ba da zai cika madatsar ruwan, don yanzu haka ma’ajiyar ruwan ko rabin cika ba ta yi ba, don su ma sun yi kokari an so a sako ruwa a hada da na Goronyo da na Talatar Mafara, amma ba zai yiwu ba saboda babu, a tsari ba a barin dam a bushe, abun da yake a cikin ma’ajiyar ruwa da shi za a yi amfani domin ma’ajiyar ta ci gaba da kasance cikin danshi, shawara guda kawai zan ba manoma musamman wadanda suke kan tudu su yi kokari wajen amfani da injunan ban ruwa, su mayar da injuna zuwa mai amfani da iskar Gas saboda yana da sauki, domin ba ya saurin konewa kamar fetur da yawa ma sun yi hakan kuma ya taimaka.” (Garba Abdullahi Bagwai)