logo

HAUSA

Antonio Guterres: Sarrafa girman tattalin arzikin Afirka ta hanyar da ta dace a manyan kungiyoyi

2023-09-22 11:56:55 CMG Hausa

A jiya Alhamis ne Antonio Guterres, Sakatare Janar na MDD a cikin wani sakon bidiyo ga shirin kasuwancin Afirka na biyu ko GABI a takaice ya ce, sarrafa damammakin Afirka zai fara ne ta hanyar samun adalci daga manyan kungiyoyi masu alaka da Afirka, musamman tsarin hada-hadar kudi na duniya.  

Ya shaida wa taron a gefen muhawarar babban taron MDD na wannan shekara cewa, Afirka na da damammaki mara iyaka, da suka hada da dimbin albarkatun kasa, da hanyoyin samar da kayayyaki zuwa ga sassan duniya, da yawan matasa masu basira, da yiwuwar zama kwandon abinci na duniya, da zama dandalin makamashi mai tsabta, haka ma yankin cinikayya maras shinge na nahiyar Afirka idan aka aiwatar da shi gaba daya zai samar da kasuwar da darajarta zai kai dalar Amurka tiriliyan 3.

"Adalci na nufin rashin zalunci da gyara tsohon tsarin hada-hadar kudi na duniya, da kuma tabbatar da wakilcin Afirka a kowane teburin tattaunawar bangarori daban-daban," a cewar babban jami'in MDD. Ya ci gaba da cewa, hakan na nufin dole ne kasashe masu ci gaba da cibiyoyin hada-hadar kudi na kasa da kasa su samar da ingantacciyar hanyar tinkarar basussuka da kuma fadada kudaden shiga na gaggawa ta yadda kasashen Afirka za su iya saka hannun jari wajen samun ci gaba mai dorewa da kuma daukar matakan da suka dace kan sauyin yanayi. (Yahaya)