logo

HAUSA

Bil adama sun bude kofar ukuba kan yanayi

2023-09-21 10:15:00 CMG Hausa

Sakatare janar na MDD Antonio Guterres, ya yi gargadin cewa, bil adama sun bude kofar ukuba kan yanayi.

Antonio Guterres ya bayyanawa taro kan burin shawo kan matsalolin yanayi da ya gudana yayin taron babban zauren majalisar cewa, tsananin zafi na yin mummunan tasiri. Manoma na kallon ambaliya tana tafiya da shukokinsu cike da damuwa, tsanantar zafi na haifar da cututtuka, kana dubban mutane na tserewa saboda tsoron gobara mafi muni a tarihi.

A cewarsa, kalubale da dama sun dankwafar da yunkurin tunkarar matsalar yanayi. Yana mai cewa, idan ba a samu sauyawar abubuwa ba, duniya za ta fuskanci karuwar digiri 2.8 na zafi wanda ke da matukar hadari. Yana mai kira da a dauki matakin domin rage karuwar zafin duniya zuwa digiri 1.5.

Ya kuma gabatar da wata yarjejeniyar hadin gwiwa kan yanayi ga manyan kasashe masu fitar da hayaki mai guba, wadanda suka fi cin gajiyar makamashin mai gurbata muhalli, da su kara kokarin rage fitar da hayakin, kana kasashe masu wadata su taimakawa kasashe masu tasowa. (Fa’iza Mustapha)