logo

HAUSA

Shugaban Ghana ya bukaci a biya diyya kan cinikin bayi

2023-09-21 10:34:22 CMG Hausa

A jiya Laraba ne shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo ya bayyana cewa, ya zama dole a biya diyya kan cinikin bayi don magance rashin adalcin tarihi da ya yi tasiri ga tsarin duniya.

Lokaci ya yi da za a amince a fili cewa yawancin kasashen Turai da Amurka an gina su ne daga dimbin arzikin da aka girbe daga gumi, hawaye, da jini da kuma ta'addancin cinikin bayi ta tekun Atlantika da kuma shekaru aru-aru da aka yi ana mulkin mallaka, shugaban ya fadi hakan ne a zaman muhawarar babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 78.

Shugaban ya ce, shekaru aru-aru, duniya ta kawar da kai game da tinkarar hakikanin illar da cinikin bayi ya haifar, amma sannu a hankali hakan yana canjawa, kuma lokaci ya yi da za a gabatar da batun diyya.

Ya kara da cewa, al’ummomin wannan zamani ba su ne suka tsunduma cikin cinikin bayi ba, amma da gangan kasashensu suka dauki nauyin wannan mummunar sana’ar, yana mai cewa fa’idar tana da nasaba da tsarin tattalin arzikin kasashen da suka tsara kuma suka aiwatar a halin yanzu. "Dole ne a biya diyya kan cinikin bayi," a cewar Akufo-Addo. (Yahaya)