An bude bikin baje kolin Sin da kasashen Larabawa karo na 6 a Yinchuan
2023-09-21 14:07:41 CMG Hausa
A yau ne, aka bude bikin baje koli na kasashen Sin da Larabawa karo na shida a birnin Yinchuan, babban birnin jihar Ningxia ta kabilar Hui mai cin gashin kanta dake yankin arewa maso yammacin kasar Sin.
Bikin na kwanaki hudu, ya samu halartar baki daga kasashe fiye da 50 irin su Saudiyya da Mauritania.
Bikin baje kolin na bana, ya kunshi baje kolin kasuwanci da tarurrukan kasuwanci da zuba jari, da aikin noma na zamani, da cinikayya tsakanin kasashe, da yawon shakatawa na al'adu, da kiwon lafiya, da sarrafa albarkatun ruwa, da hadin gwiwa kan nazarin yanayi.
Fadin filin baje kolin ya kai kusan murabba'in mita dubu 40, yayin da sama da kamfanoni na cikin gida da na waje dubu guda suka halarci baje kolin.
Bikin da aka fara gudanarwa a shekarar 2013, ya zama wani muhimmin dandali ga kasashen Sin da Larabawa, don sa kaimi ga yin hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare, da inganta hadin gwiwar shawarar “ziri daya da hanya daya”.
A halin yanzu kasar Sin ce babbar abokiyar cinikayyar kasashen Larabawa, kuma adadin cinikayya tsakanin sassan biyu, ya kusan ninkawa sau biyu daga matakin shekarar 2012 zuwa dalar Amurka biliyan 431.4 a bara. A cikin watanni 6 na farkon bana, ciniki tsakanin Sin da kasashen Larabawa ya kai dalar Amurka biliyan 199.9. (Ibrahim)