logo

HAUSA

Gwamnatin jihar Adamawa za ta hada wasu garuruwa 7 da wutan lantarki

2023-09-21 09:46:03 CMG Hausa

Majalissar zartaswa ta jihar Adamawa ta amince da fitar da kudade masu yawan gaske domin karasa ayyukan wutan lantarki a wasu gururuwa 7 dake yankin karamar hukumar Gombi.

Kwamishinar yada labaran jihar Mrs Neido Geoffrey Kofulto ce ta tabbatar da hakan ga manema labarai jim kadan da kammala taron majalissar kwamishinonin jihar da aka gudanar karkashin jagorancin gwamnan jihar Ahmadu Fintiri. Ta ce an bayar da ayyukan ne tun a shakara ta 2007, amma aka yi watsi da shi ba tare da an ci kaso 20 na adadinsa ba.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Mrs Neido Kofulto ta ce, tun a wancan lokaci dai an bayar da kwangilar ayyukan ne a kan kudi sama da Naira miliyan 44, amma yanzu farashin aikin ya ninka sosai, sai dai duk da haka gwamnati ta sha alwashin ganin an kammala aikin domin dai jin dadin al’ummar yankunan.

Ta ce kwamasinan ma’aikatar raya karkara na jihar ne ya gabatar da bukatar karasa ayyyukan, bayan kuma nazarin da aka yi tare da daidaita farashin aikin ta yadda zai dace da yanayin tattalin arzikin da ake ciki a halin yanzu, gwamnati ta amince da bukatar ba tare da doguwar muhawara ba.

“A yanzu haka majalissar zartaswar ta amince da fitar da tsabar kudi naira miliyan dari da casa’in da biyu da dubu dari shidda da saba’in da shidda da naira dari biyu da hamsin da tara da kwabo goma a matsayin kudin sabunta kwangilar ayyukan a yankin karamar hukumar Gombi.”

Kwamashinar ta ce aikin yana cikin kasafin kudin shekarar 2023 da aka amince da shi karkashin ayyukan da za a yi, kuma nan ba da jimawa ba, za a fara gudanar da aikin saboda tuni majalissar zartaswar jihar ta sahale. (Garba Abdullahi Bagwai)