Sin ta sanya hannu kan yarjejeniyar kare mabanbantan halittun teku
2023-09-21 21:18:39 CMG Hausa
A jiya Laraba ne mataimakin ministan ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Ma Zhaoxu, ya sanya hannu kan yarjejeniyar karewa, da wanzar da amfani da mabanbantan albarkatun halittun teku a matakin kasa da kasa, karkashin yarjejeniyar MDD mai alaka da kare teku. Ma ya sanya hannu kan yarjejeniyar ne a madadin gwamnatin kasar Sin, a helkwatar MDD dake birnin New York.
Yarjejeniyar ta kunshi mallaka, da rarraba albarkatun asalin halittun teku, da kafa yankin kare halittun teku, da aiwatar da binciken yanayin muhalli, da gina kwarewa, da gabatar da fasahohin teku, duka dai da nufin kara kafa ka’idojin jagorancin albarkatun teku na duniya. (Saminu Alhassan)