logo

HAUSA

Sin da kasashe masu ra’ayi iri daya sun yi kira da a inganta rayuwar mata masu bukata ta musamman a cikin al’umma

2023-09-21 10:26:19 CMG Hausa

A jiya ne, kasar Sin da kasashe masu ra’ayi iri daya, suka bayyana muhimmancin inganta rayuwar al'ummomi, ta yadda hakan zai amfani mata masu bukata ta musamman, da yadda za su ba da gudummawarsu ga rayuwarsu da ma ci gabansu.

A yayin da yake jawabi a wajen taron hukumar kare hakkin bil Adama karo na 54 da gudana a halin yanzu, shugaban tawagar kasar Sin a ofishin MDD dake Geneva Chen Xu, ya bayyana cewa, mata masu nakasa daidai suke da kowane dan Adam.

A madadin kasashe sama da 80, Chen ya bayyana a cikin wata sanarwar ta hadin gwiwa cewa, tun bayan da aka gudanar da taron mata na duniya karo na hudu a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, manufar ci gaban mata a duniya ta bunkasa matuka. Amma duk da haka, mata masu nakasa suna fuskantar matsaloli, kamar rashin ingantaccen tsaro, da yadda ake nuna musu wariya da kuma matsalar talauci.

Sanarwar ta yi kira ga kasashen duniya, da su kara ilimantar da jama'a game da cudanya da jama'a, da yin kokarin kawar da kyama da nuna wariya ga mata masu nakasa.

Sanarwar ta kara da cewa, adadin mata masu nakasa da ake dauka aiki, bai kai na dukkan rukunin mutane masu nakasa da mata ba. Don haka sanarwar hadin gwiwar ta jaddada cewa, akwai bukatar a yi kokarin saukaka ci gabansu da ma makomarsu baki daya, ta yadda za a inganta ’yancinsu na rayuwa da ci gaba, da ciyar da su gaba da ba su kariya yadda ya kamata. (Ibrahim Yaya)