Han Zheng ya yi kira ga Sin da Amurka da su kyautata matakan shawo kan sabani
2023-09-21 19:56:00 CMG Hausa
Mataimakin shugaban kasar Sin Han Zheng, ya ce a matsayin Sin na babbar kasa mai tasowa, da Amurka dake matsayin babbar kasa mai wadata, kamata ya yi su karfafa tattaunawa, tare da kyautata matakan su na shawo kan sabanin dake tsakaninsu yadda ya kamata.
Han Zheng, wanda ya bayyana hakan a jiya Laraba, yayin ganawarsa da jagororin kungiyoyin kawance na Amurka, da kwararru, da sauran mutane daga sassan rayuwa mabanbanta, a gefen taron kolin MDD dake gudana yanzu haka a birnin New York, ya yi kira ga sassan biyu da su nacewa manufofin nan 3 na mutunta juna, da zaman jituwa, da hadin gwiwar cimma moriya tare, wadanda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, kana su aiwatar da muhimmiyar yarjejeniyar da shugabannin kasashen 2 suka amincewa, yayin taron Bali na kasar Indonesia. (Saminu Alhassan)