logo

HAUSA

Yanayin gasar wasannin motsa jiki ta kasashen Asiya karo na 19 na kara yaduwa a birnin Hangzhou

2023-09-20 15:22:59 CMG Hausa

Yayin da gasar wasannin motsa jiki ta kasashen Asiya karo na 19 wato Asian Games ke gabatowa, ana kara samun mutanen dake nuna sha’awar wasannin motsa jiki a Hangzhou, wato birnin da zai karbi bakuncin gasar. Cibiyar wasannin al’adu da motsa jiki dake yankin Xihu, daya ne daga cikin wuraren motsa jiki da mazauna birnin Hangzhou ke son zuwa, ganin yadda yake da girma wanda ke shafar fannoni daban-daban.