logo

HAUSA

Najeriya za ta hada hannu da kasar Benin wajen dakile shige da ficen haramtattun kayayyaki da ayyukan ta’addanci a kan iyakoki

2023-09-20 09:18:43 CMG Hausa

Hukumar Kwastam mai lura da shige da ficen kayayyaki a tarayyar Najeriya ta jaddada aniyarta na yin aiki tare da takwararta ta jamhuriyar Benin wajen kyautata sha’anin tsaro a kan iyakoki tare da daidaita harkokin cinikayya a tsakanin kasashen biyu.

Babban kwantrolan hukumar Mr. Bashir Adewale Adeniyi ne ya tabbatar da hakan a birnin Abuja lokacin da yake karbar bakuncin manyan jami’an hukumar kwastam na jamhuriyyar Benin karkashin jagorancin darakta janaral na hukumar Mr. Alain Hinkati, inda ya ce, Najeriya da jamhuriyyar Benin suna lura da kan iyakoki masu matukar muhimmanci da tasirin gaske ga sha’anin tattalin arziki da kuma tsaro a nahiyar Afrika baki daya.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdulahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Shugaban hukumar kwastam na tarayyar Najeriya wanda yake jawabi yayin taron hadin gwiwa tsakanin wakilan kasar ta Benin, ya ce akwai dadadiyar alaka ta cinikayya da al’adu a tsakanin Najeriya da jamhuriyar Benin, kuma bai kamata ba a bari masu fasa kaurin haramtattun kayayyaki su sukurkutar da wannan alaka.

Mr Bashir Adeniyi ya ci gaba da cewa,“Wannan ziyara da takwarorinmu na jamhuriyar Benin suka kawo mana zai samar da muhimmiyar dama na samun nasarar tattaunawar da muke kan yi a halin yanzu ta yadda za mu daidaita tsarin ayyukanmu ya tafi tare da na hukumar kwastam ta jamhuriyar Benin. A dan wannan kwarya-kwaryar taro da muka gudanar mun fara lalubon bakin zaren yadda za mu lura da yadda masu shigo da kayan ke amfani da tasoshin ruwanmu, da kuma batun sake duba kayayyakin da kasashen biyu suka haramta shigowa da su. Sai kuma abu na karshe nazari kan yawan kiraye-kirayen da ake mana na neman bukatar sake duba batun rufe wasu tasoshin dake kan iyakoki.” 

A jawabinsa darakta janaral na hukumar kwastam ta jamhuriyar Benin Mr. Alain Hinkati fata ya yi na cewa, taron nasu zai kawo karshen matsalolin cinikayya da ake fuskanta tsakanin kasarsa da Najeriya, tare da fito da wani sahihin tsari da zai yi jagora wajen aiwatar da sabbin matakai da za su inganta harkokin kudaden shiga a tsakanin kasashen biyu. (Garba Abdullahi Bagwai)