logo

HAUSA

Masanin kasar Sin ya soki matakin Japan na zuba dagwalon tashar Fukushima cikin teku

2023-09-20 11:09:06 CMG Hausa

Masani dan kasar Sin Li Shouping, ya ce hakkokin muhalli da mutane ke mora, suna cikin daukacin hakkoki bil adama, kuma zubarwa da sarrafa abubuwa masu hadari, ba batu ne da kasa daya tilo ke da iko a kai ba.

Li Shouping, wanda masani ne daga kungiyar nazarin hakkokin bil adama ta kasar Sin, kuma farfesa a kwalejin nazarin fasaha ta Beijing, shi ne wakilin musamman na MDD kan tasirin hakkokin bil adama dangane da kula da muhalli da zubar da gurbatattun abubuwa da shara. Ya bayyana haka ne jiya Talata, ga zaman taro na 54 na majalisar kare hakkokin bil adama ta MDD dake gudana.

A ranar 24 ga watan Augusta ne, gwamnatin Japan ta zuba gurbataccen ruwun nukiliya da ya fito da lalatacciyar tashar nukiliya ta Fukushima a cikin teku, duk da shakku da adawa mai karfi da al’ummomin kasa da kasa suka nuna.

A cewarsa masanin, abun da Japan ta yi, tura hadari ne ga duniya, da kai illolin ga zuri’o’i na gaba, da kuma mayar da kanta mai lahanta muhallin hallitu, kuma mai gurba muhallin teku. (Fa’iza Mustapha)