logo

HAUSA

Shugaban Afrika ta kudu ya soki yadda ake zuba kudi a yaki maimakon kyautata rayuwar jama’a

2023-09-20 11:11:18 CMG Hausa

Shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa, ya soki yadda ake zuba wajen yaki maimakon inganta rayuwar jama’a.

Cyril Ramaphosa ya bayyana haka ne ga taron muhawarar babban zauren MDD. Yana mai cewa, babban laifi ne yadda kasashen duniya ke kashe makudan kudi kan yaki, amma ba za a iya tallafawa ayyukan da za su biya muhimman bukatun biliyoyin jama’a ba.

Ya ce a wannan lokaci da ya kamata kowa ya mayar da hankali ga kokarin cimma ajanadar 2030, hankali ya karkata saboda radadin yaki. 

Ya ce kasa da kasa na da dama da ikon tunkara da shawo kan manyan kalubalen da bil adama ke fuskanta yanzu haka. Yana mai kira ga kasashen duniya su nuna kuduri da niyyar samar da zaman lafiya da ci gaba da kyakkaywar makoma ga duniya da zuri’o’i na gaba. (Fa’iza Mustapha)