logo

HAUSA

Indiya ta kori babban jami’in diflomasiyyar Canada

2023-09-20 16:12:39 CMG Hausa

Gwamnatin Indiya ta kori wani babban jami’in diflomasiyyar kasar Canadaa ranar Talata, inda ta nemi ya bar kasar cikin kwanaki biyar masu zuwa.

Matakin ya zo ne bayan da Ottawa ta kori wani jami’in diflomasiyyar Indiya bisa zariginsa da hannu a kisan jagoran mabiyan addinin Sikh na Canada Hardeep Singh Nijjar a farkon wannan shekara. An kashe Nijjar a Surrey, lardin British Columbia na Canada, a ranar 18 ga Yuni.

Sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen Indiya ta fitar ta ce, matakin ya nuna yadda gwamnatin Indiya ke kara nuna damuwarta kan tsoma bakin jami'an diflomasiyyar Canada a cikin harkokin cikin gidan Indiya da kuma yadda suke shiga cikin harkokin da suka shafi kasar Indiya. (Yahaya)