Han Zheng: Sin za ta yi hadin gwiwa da Guinea wajen kare moriyar kasashe masu tasowa
2023-09-20 19:35:17 CMG Hausa
Mataimakin shugaban kasar Sin Han Zheng, ya ce kasar sa a shirye take ta yi hadin gwiwa da Guinea, wajen goyon bayan juna, a batutuwan da suka jibanci kare muhimman moriyar su, tare da kare muradun sauran kasashe masu tasowa.
Han ya yi wannan alkawari ne a jiya Talata, lokacin da yake zantawa da shugaban rikon kwaryan Guinea Mamady Doumbouya, a gefen taron muhawara, a babban zauren MDD dake gudana a birnin New York.
Kaza lika, a cewar mataimakin shugaban kasar Sin, kasar sa na jinjinawa Guinea, bisa shiga rukunin masu goya bayan shawarar bunkasa duniya, kana Sin din ta shirya tafiya tare da Guinea, wajen ingiza kawancen gargajiya dake tsakanin su, da fadada cimma moriyar juna, da kara zurfafawa, da kafafa kyakkyawar dangantakar sassan 2. (Saminu Alhassan)