logo

HAUSA

An fara muhawara a babban zauren MDD

2023-09-20 10:48:21 CMG Hausa

An fara muhawara ta babban zauren MDD karo na 78 a hedkwatar majalisar dake birnin New York na Amurka a jiya, inda aka mayar da hankali kan farfado da aminci a duniya da hadin gwiwa a wannan lokaci da ake fuskantar kalubale.

Shugaban zauren MDD na 78 Dennis Francis, shi ne ya shugabanci bude muhawarar mai taken “Sake gina aminci da farfado da hadin gwiwar duniya: gaggauta daukar mataki kan ajandar 2030 da muradun ci gaba masu dorewa domin samun zaman lafiya da wadata da ci gaba da jituwa tsakanin halittu”. 

A rahoton da ya fitar kan yanayin duniya, kafin bude muhawarar ta bana, sakatare janar na MDD Antonio Guterres ya yi kira ga hukumomin kasa da kasa da su warware kalubalen da duniya ke fuskanta. Yana mai gargadin duniya na cikin matsanancin yanayi.

Ya kuma yi kira da a jajirce wajen daukaka ka’idojin MDD na tabbatar da zaman lafiya da yi wa cibiyoyin hada-hadar kudi gyaran fuska. Ya kara da yin kira da a shawo kan barazanar da bil adama ke fuskanta yanzu haka, wato dumamar yanayi. 

Har ila yau, ya yi kira da a jajirce wajen martaba ka’aidojin majalisar na kare hakkokin bil adama, cikinsu har da hakkokin mata. (Fa’iza Mustapha)