logo

HAUSA

Sin Tana Nacewa Ga Matsayin Ta A Rukunin Kasashen “Global South”

2023-09-20 21:25:01 CMG HAUSA

DAGA CMG HAUSA

A gun babban taron MDD karo na 78 da ake gudanarwa, damuwar kasashe masu sabbin kasuwanni da kasashe maso tasowa ko “Global South”, ta zama muhimmin batun tattaunawa.

A shekarun baya bayan nan, kasashen yamma musamman ma Amurka, sun yi ta yunkurin ware Sin daga rukunin “Global South”, don haifar da baraka ga kasashe maso tasowa, da kiyaye moriyar kasashe masu wadata.

Shin ko za su iya cimma nasara? Taron koli na kungiyar kasashe 77 da Sin sun ba da amsa, inda taron ya zartas da sanarwar Havana, wadda ta shigar da ra’ayi, da matsayin Sin da dama. Wannan shi ne kwarin gwiwar da kasashen “Global South” suka bayyana, kuma ya nuna cewa, Sin na cikin rukunin kasashe masu sabbin kasuwanni da kasashe maso tasowa ko “Global South”.   (Amina Xu)