Gasar nuna gwaninta kan sana’a ta kasar Sin ta mai da hankali kan fasahohin musamman
2023-09-20 10:11:42 CMG Hausa
Masu kallonmu, barkanmu da war haka! Kwanan baya, an bude gasar nuna gwaninta kan sana’a ta kasar Sin karo na biyu a birnin Tianjin da ke arewacin kasar Sin, inda kwararru a fannoni daban daban sama da dubu 4 daga sassan kasar Sin suka halarci gasar, domin cimma nasarori cikin gasanni 109.