Han Zheng: Sin na fatan hada gwiwa da sauran sassa wajen ingiza shawarar bunkasa duniya
2023-09-20 20:31:45 CMG Hausa
Mataimakin shugaban kasar Sin Han Zheng, ya ce Sin a shirye take ta yi aiki tare da sauran sassa, wajen ingiza kyakkyawan yanayin cimma nasarar shawarar nan ta bunkasa duniya ko GDI.
Han Zheng, ya bayyana hakan ne a jiya Talata, yayin babban taron nazarin nasarar da aka cimma, a fannin hadin gwiwar raya shawarar ta GDI, a taron da kasar Sin ta jagoranta, a gefen taron kolin MDD na bana.
Kaza lika a cewar sa, bangaren Sin na fatan shiga a dama da shi wajen aiwatar da ajandar ci gaba mai dorewa ta MDD ta nan da shekarar 2030, tare da gina al’ummar duniya mai ci gaban bai daya.
Shawarar GDI, wadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar yayin taron kolin MDD karo 76 a shekarar 2021, na da nufin cimma daidaito tsakanin sassan kasa da kasa, a fannin ingiza ci gaba, da fadada bunkasuwar bai daya ta dukkanin kasashen duniya. (Saminu Alhassan)