Ya kamata a kare hakkin wadanda masu bukata ta musamman
2023-09-20 08:35:08 CMG Hausa
Kimanin mutane biliyan 1.3, ko kashi 16% na al'ummar duniya suke fama da lallaurar gabobin jiki wanda ya sanya su zama masu bukata ta musamman. Wannan adadin na karuwa ne saboda karuwar cututtuka da kuma yawan shekaru ko kuma a sanadin hadari. Wadannan mutane masu bukata ta musamman sun kasu cikin rukuni daban-daban, kuma dalilai kamar shekaru, asalin jinsi, addini, kabila da yanayin tattalin arzikinsu yana shafar bukatunsu na yau da kullun. Kaza lika, suna fuskantar gazawa a cikin ayyukan yau da kullun wanda ya sanya su zama mutane masu bukata ta musamman. Suna da karancin lafiyar jiki, kana suna mutuwa da wuri.
Kididdigar da kungiyar masu bukata ta musamman ta kasar Sin ta fitar a bara ta nuna cewa, akwai masu bukata ta musamman sama da miliyan 85 a kasar Sin, wanda ya kai fiye da kashi 6.3 na yawan jama'ar kasar. Kulawa da bukatun wadannan mutane na musamman na daya daga cikin muhimman manufofin kasar Sin, wanda hakan ya sanya su hadewa waje guda a matsayin kungiya a hukumance, suke gabatar da bukatunsu ga gwamnati da murya daya, yayin da suka gudanar da taronsu na kasa karo na takwas, a ranar Litinin 18 ga watan Satumba a nan birnin Beijing.
Masu bukata ta musamman na bukatar karin kariya da taimako daga hukumomi duk da irin ci gaban da kasar Sin ta samu wajen kyautata yanayinsu. Duk da haka, ya kamata a ci gaba da yin taka-tsan-tsan don taimakawa wajen rage talauci a tsakaninsu.
Mata da maza masu masu wannan lallurar su ma suna daga cikin al'umma. Kasashe masu tasowa na kokarin habaka karin kungiyoyin jama'a don samar da guraben aikin yi a gare su, da damar samun ingantaccen ilimi na asali, horo da sana'o'in da suka dace da bukatun kasuwancin kwadago da ayyukan da suka dace da kwarewarsu. Yawancin al'ummomi sun fara fahimtar bukatar wargaza wasu shingaye da ke hana masu bukata ta musamman samun ci gaba a rayuwa. (Mohammed Yahaya, Saminu Alhassan, Sanusi Chen)