logo

HAUSA

A Daɗe Ana Yi Sai Gaskiya

2023-09-19 19:49:19 CMG HAUSA

DAGA YAHAYA

Shekarar 2023 ta cika shekaru 20 da kulla dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da ƙungiyar ASEAN wato ƙungiyar ƙasashen kudu maso gabashin Asiya, da kuma cika shekaru 20 da kafuwar baje kolin Sin da ASEAN. Wannan ya ba da muhimmiyar ma'ana ga bikin baje kolin Sin da ASEAN na bana, wanda aka bude a ranar 17 ga watan Satumba a birnin Nanning na jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai cin gashin kanta ta kudancin ƙasar Sin.

 

Ƙasar Sin ta ci gaba da rike matsayinta na babbar abokiyar hulɗar kasuwanci ta ASEAN tsawon shekaru 14 a jere, kuma ɓangarorin biyu sun kasance manyan abokan harkalla a fannin cinikayya mafi girma cikin shekaru uku a jere tun daga shekarar 2020. An kara inganta aikin gina yankin cinikayya maras shinge na ƙasar Sin da ASEAN, tare da ƙara ƙarfafa matsayin Sin da ASEAN a matsayin manyan abokan cinikayyar juna.  A cikin ’yan shekarun nan, ƙasar Sin ta zama muhimmiyar ƙasa mai saka hannun jari a ƙasashen waje ga ƙasashen ASEAN.    

 

An ci gajiyar bikin baje koli na ƙasar Sin da ASEAN da kuma taron kolin harkokin kasuwanci, haɗin gwiwar tattalin arziki tsakanin ƙasashen ASEAN da ƙasar Sin sun haɓaka daga ingantacciyar cinikayya da zuba jari zuwa haɗin gwiwar ƙarfin samar da kayayyaki na ƙasa da ƙasa, da harkokin kuɗi, da tattalin arziki na fasahar zamani ko dijital, da kiwon lafiya, da yawon buɗe ido, da ilimi da dai sauransu.  Haɗin gwiwar dake tsakanin ɓangarorin biyu na da matuƙar tasiri.

 

Baje kolin ya ba da dama ga kasashen ASEAN don faɗaɗa fitar da kayayyaki masu inganci da fa'ida zuwa ƙasar Sin, da faɗaɗa cinikayya ta hanyar buɗe sabbin kasuwanni. Kana, zai taimaka wajen ba da gudummawa ga daidaiton ci gaban cinikayya tsakanin Sin da ASEAN.

 

Baje kolin bana ya zama wani abin ƙarfafa gwiwa ga gina yankin cinikayya maras shinge na Sin da ASEAN (FTA). A bukukuwan baje koli na ƙasar Sin da ASEAN na shekarun da suka gabata, an kiyasta cewa 'yan kasuwa fiye da miliyan 1.1 ne suka halarci bukukuwan baje kolin a jimlance. Ana sa ran baje kolin bana wanda shi ne karo na 20 zai samu halartar ƙasashe fiye da 40 da kuma masu baje koli kusan 1,700.   

 

Ga ƙasashen ASEAN, bikin baje kolin wani muhimmin al'amari ne na bunƙasa harkokin cinikayya, zuba jari, da musayar kayayyaki da yawon buɗe ido, wanda zai taimaka wajen ƙarfafa hulɗar tattalin arziki da cinikayya tsakanin ƙasashen Asiya da Sin da sauran ƙasashen yankin, da ƙara yin la'akari da damar da aka samu da aiwatar da yankin cinikayya maras shinge na ƙasar Sin da ASEAN. 

 

A bana, masu baje koli kusan 640 daga ƙasashen ASEAN za su baje kolin hajojinsu da suka hada da biscuits, kofi, koko da cakulan da aka yi a ASEAN, da ruwan 'ya'yan itace ko lemo, da kayan marmari da sauran abinci na musamman. kaza lika, za a yi nune-nunen tufafin sakawa, kayan ado irin su sarka, awarwaro, da ababe masu inganta lafiya da kyawun jiki, da sauran kayayyaki na musamman daga ƙasashen ASEAN.

 

Kamfanoni 120 na Vietnam za su baje kolin kayayyakin gona, da kayan ruwa, da abinci da aka sarrafa, da kayayyakin amfanin gida, yadi da tufafi, da kayayyakin ƙawata gida da aka kera da katako kaman kujeru da gadaje da dai sauransu. Kamfanonin Singapore 23 ne za su halarci baje kolin kuma za su gudanar da ayyukan zuba jari da ci gaban kasuwanci sama da 70.

 

A gefen bikin baje kolin, za a gudanar da taron baje kolin hadin gwiwar zuba jari, da taron zuba jari na masana'antu na ASEAN, da taron daidaita ayyuka, wani taron musamman kan zuba hannun jari a Sin wato "Invest in China Year–Enter Guangxi" a Turance, da dai sauransu, wadannan tarukan za su gudana ne don zurfafa hadin gwiwar tattalin arziki, cinikayya da zuba jari tsakanin Sin da ƙasashen ASEAN. (Yahaya)