logo

HAUSA

Wang Yi ya bukaci Sin da Rasha su nacewa tsarin cudanyar sassa daban daban bisa gaskiya

2023-09-19 19:49:40 CMG Hausa

Ministan ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya ce yayin da duniya ke fama da karuwar akidun ware kai, da danniya, da fito na fito, kamata ya yi Sin da Rasha su nacewa tsarin cudanyar sassa daban daban bisa gaskiya.

Wang Yi, wanda ya bayyana hakan a jiya Litinin, yayin da yake zantawa da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov, ya ce kamata ya yi kasashen biyu su rungumi yanayin da ya dace da zamani, su sauke nauyin dake wuyan su, kasancewar su manyan kasashen duniya, kana su cika alkawuran su a fagen cudanyar kasa da kasa. (Saminu Alhassan)