logo

HAUSA

Shugabannin duniya sun sake jaddada aniyarsu ga SDGs

2023-09-19 10:24:10 CMG Hausa

A jiya Litinin ne shugabannin kasashen duniya suka sake jaddada aniyarsu ta cimma muradun ci gaba masu dorewa (SDGs) a taron koli na SDG, wanda ke gudana a gefen muhawarar babban taron MDD na bana. 

A cikin sanarwa ta siyasar da aka amince da su a taron, shugabannin sun sake jaddada aniyarsu ta “aiwatar da ajendar 2030 da tsare-tsaren SDG yadda ya kamata tare da kiyaye dukkan ka’idojin da aka gindaya a ciki”.

Shugabannin sun jaddada cewa, kawar da talauci shi ne babban kalubale a duniya kuma abu ne mai muhimmanci ga ci gaba mai dorewa.

Shugabannin sun yi alkawarin inganta "mai da hankali zuwa ga samar da duniya mai cike da adalci, zaman lafiya, juriya da dorewa ga mutane da duniya, na yanzu da na zamani mai zuwa”. (Mohammed Baba Yahaya)