logo

HAUSA

Gwamnatin Kano na shirin sarrafa shara zuwa taki

2023-09-19 09:21:31 CMG Hausa

Gwamnatin jihar Kano dake arewacin Najeriya ta fara tattaunawa da wasu kamfanonin cikin gida da na kasashen waje domin duba yiwuwar sarrafa sharar da ake samu a jihar zuwa takin zamani.

Gwamnan jihar Injiniya Abba Kabir Yusuf ne ya tabbatar da hakan lokacin da yake kaddamar da gangamin yaki da  tarin sharar dake jibge a sassan dake cikin birnin Kano. Ya ce, yanzu lokaci ya wuce da za a rinka zubar da shara a ramuka, akwai bukatar a alkinta ta domin a rinka cin moriyarta. 

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Domin cimma burin gwamnatin na tsaftace birnin Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya ce, gwamnatinsa ta debi matasa 4,500 da za su rinka aikin share titunan dake cikin birnin Kano.

Haka kuma ya bayyana cewa, a yanzu haka gwamnati ta sake yin odar manyan motocin tifa na kwashe shara har guda 10, sannan kuma an gyara wasu da dama da suka lalace.

Injiniya Abba Kabir Yusuf ya ce, jihar Kano wadda ta fi kowacce jihar a Najeriya cunkoson jama’a, tana samar da sharar da ta kai tan dubu 150 a kowacce rana, inda ya ce, wannan babbar kadara ce da za ta amfani al’umma da tattalin arzikin jihar Kano idan har an alkinta ta yadda ya kamata.

“A duniya yanzu abun da ake yi shi ne ana sarrafa wannan shara daga sharar juji ta kazanta tana komawa takin zamani wanda ake amfani da shi a gonaki, gwamnatin jihar Kano tana nan tana shiri da wata kasa da wasu mutane da za su kawo injina, wadannan injina za a dinga kwashe shara ana kaiwa wannan wuri, su kuma injina ana zuba masu sinadarai suna canjawa suna komawa takin zamani. Abun jin dadin ma a nan shi ne ban da samun takin zamani da za a yi, abun mafi muhimmanci kuma shi ne matasanmu za su samu ayyukan yi.”

Gwamnan jihar ta Kano ya tabbatar da cewa, shirye-shirye sun yi nisa wajen kulla yarjejeniyar fahimtar juna da kamfanoni mallakin ’yan kasa da kuma na kasashen waje domin fara sarrafa shara zuwa taki a jihar Kano. Lamarin da zai kara kyautata sha’anin kudaden shiga da kuma samun ingantaccen muhalli domin ci gaba rayuwar al’umamr jihar baki daya. (Garba Abdullahi Bagwai)