“Mafarkina na zuwa sararin samaniya”:Bayyana mafarkin matasan Sin da Afirka ta hanyar zane-zane
2023-09-19 17:44:43 CMG Hausa
A cikin dogon tarihin bil’adama, binciken sararin samaniya bai taba tsayawa ba, kuma matasa su ne babban karfin binciken sararin samaniya da kuma makomar sana’ar sararin samaniyar bil’adama. A kasashen nahiyar Afirka, akwai wasu matasa, wadanda suka zana mafarkinsu na sararin samaniya, kuma 'yan saman jannatin kasar Sin sun taimaka musu wajen cimma burinsu. A cikin shirinmu na yau, za mu ji yadda 'yan saman jannatin kasar Sin sun taimaka musu wajen cimma burinsu.