logo

HAUSA

Me ya sa ake yawan samun laifukan fashi a Amurka?

2023-09-19 14:04:31 CMG

Gungun mutane sun hadu ta shafin kafar sada zumunta, sa’an nan suka hadu a zahiri sun kutsa cikin shaguna sun yi fashi, sa’an nan suka bar shagunan a barkatai. Wannan hali na fashi a fili a matsayin 'sayayya ba tare da ko sisi ba' ya zama abin ba'a ga Amurkawa, a baya wannan salo na daukar abu a shago ba tare da biyar kudi ba ya kasance wata dabara ga ‘yan kasuwa wajen tallata kayayyakinsu, amma yanzu ta zame musu ciwon kai.

Alkaluman da kungiyar masu cinikin sodore ta kasar Amurka ta samar sun shaida cewa, a shekarar 2022, laifukan da aka aikata wa masu cinikin sodore ya karu da kashi 26.5% kwatankwacin na shekarar 2021. Duk da yawan laifukan fashi da ake aikatawa, amma sashen ‘yan sanda na kasar na fuskantar matsalar “karancin ma’aikata”, matakin da ya sa suka kasa kara karfin tinkarar matsalar.

To, amma me ya sa ake yawan samun laifukan fashi a kasar Amurka? Mun dai yi bincike a kan rahotannin da kafofin yada labarai na kasar Amurka suka bayar game da laifukan fashi da aka aikata tun farkon bana, inda muka gano cewa, yawan laifukan ya kai matsayin koli a watan Agusta. Sai kuma alkaluman da ma’aikatar kwadago ta kasar ta bayar sun shaida cewa, yawan rashin aikin yi a watan Agusta a kasar ta Amurka ya karu da kaso 0.3% kwatankwacin na watan Yuli, adadin da ya kai matsayin koli tun bayan watan Faburairun bana, wato akasin yadda kyakkyawan yanayin tattalin arziki da Amurka ta bayyana take ciki, don haka ma, lamarin ya janyo cece-kuce a tsakanin al’umma game da ko tattalin arzikin Amurka na cikin yanayi mai kyau ko a’a.

Manazarta sun kuma yi nuni da cewa, yawan laifukan fashi sun nuna babban gibi tsakanin matalauta da ma masu kudi na kasar, duk da cewa kasar ta jari hujja ce mafi karfi a duniya.(Lubabatu)