logo

HAUSA

Duan Yiran: ‘Yar kabilar Bai da ke himmatuwa wajen yayata fasahar rini a kasar Birtaniya

2023-09-18 21:16:58 CMG Hausa


Tun daga shekarar 2019 da ta kafa kamfanin Yicrafts, Duan Yiran, matashiyar Basiniya ‘yar kabilar Bai, ke yayata fasahar rini a birnin London na Birtaniya. Ta ce abu mafi muhimmanci a aikin fasahar hannu ba kammala aikin ba ne, amfani da wannan fasaha wajen hada mutane masu al’adu daban-daban shi ne abu mafi muhimmanci.

Duan ‘yar yankin Dali na kabilar Bai mai zaman kansa ne dake lardin Yunan na kudu maso yammacin kasar Sin. Lardin dake da mafi yawan kananan kabilu a kasar. Akwai kimanin kananan kabilu 25 a lardin Yunan. Sama da rabin al’ummar yankin Dali, ‘yan kabilar Bai ne.

A shekarar 2019, bayan ta kammala karatu a makarantar nazarin wasan kwaikwayo da gabatar da jawabi ta jami’ar London, inda ta nazarci tsarin kwalliyar tufafi, sai Duan ta kafa wani dakin nune-nune mai suna Yicrafts, domin koyar da fasahohin hannu na gargajiya na kasar Sin kamar rini da surfani da saka.

Da farko, mutane kalilan ne kan ziyarci wurin, kuma galibinsu tsoffin malamanta ne da abokan karatu. Duan, ta samar da wani bidiyo dake nuna yadda ake rini irin na kabilar Bai, haka kuma ta fara gabatar da kwasa-kwasai ta intanet a dandalin sada zumunta na Birtaniya, domin ta gabatar da wadannan fasahohi.

Kwalliya ta biya kudin sabulu. Yicrafts ya yi fice, ya zama sananne tsakanin jama’ar London, da kuma wasu kasashe.

Dakin ya ci gaba da kyautata hulda da hadin gwiwa da makarantu da kamfanoni da cibiyoyi a London. Misali, ya shirya taron karawa juna sani da jami’ar London da gidan adana kayayyakin tarihi na Victoria and Albert.

Duan ta bayyana cewa, “a shekarar 2021, dakin nune-nune na Walt Disney Animation ya gayyace mu zuwa wani taron karawa juna sani kan sakar gora ga ayarin shirin The Raya and the Last Dragon na 2021, domin akwai wani babi cikin shirin da ya kunshi sakar gora.” 

Taken Yicrafts shi ne, “Fasahohin hannu, al’adu da rayuwa a hankali”. Duan kan karbi duk wanda ya ziyarci wurin nata cikin karamci.

Da aka tambaye ta dalilin da ya sa take gudanar da sana’ar fasahohin kasar Sin a London, Duan ta ce, hakan na da alaka sosai da iyalinta da kuma wurin da ta taso.

Ta ce, “a lokacin da nake tsara fasalin kayayyakin na lokacin mulkin Sarauniya Victoria, na yi amfani da wasu dabarun surfani da saka da na koya daga kakata. Malamaina na ganin shi a matsayin mai ban sha’awa, kuma sun ce ni ce dalibarsu ta farko da ta tsara tufafi da fasahar gargajiya ta wata kabila.”

An haifi Duan a kauyen Zhoucheng na garin Xizhou dake yankin Dali. Kauyen ya yi fice a matsayin “garin rini na kabilar Bai”, haka kuma sananne ne a fannin dabarun rini na kabilar Bai. Wadannan dabaru sun samo asali ne tun daga lokacin karshen daular Ming, wato kimanin shekaru 480 da suka gabata.

A shekarar 2006, fasahar rini ta kabilar Bai ta shiga cikin jerin sunayen al’adun gargajiya da ba na kayayyaki ba da aka yi gado daga kakanni kakanni da majalisar gudanarwar kasar Sin ta amince da su. 

Zuri’a 4 na iyalin Duan ne suka yi ta gadon wannan fasaha ta rini. Bisa la’akari da cewa iyalinta na da wani shagon rini, Duan ta fara taimakawa ta hanyar gudanar da ayyuka masu sauki, tun tana karama iyalinta suke gudanar da sana’ar rini.

Duan ta bayyana cewa, “kusan dukkan gidajen dake kauyenmu suna aikin rini, inda galibinsu suka kasance mutanen da suka manyanta. Ina ganin yadda suke rini a kullum a lokacin da nake karama, kuma da kaina na koyi wasu ayyukan.”

Kakan Duan na da wani gidan sayar da shayi a yankin Dali, kuma gidan ya yi fice tsakanin masu yawon bude ido na cikin gida da na ketare. Daga baya, mahaifin Duan ya sauya wannan wuri na sayar da shayi zuwa gidan sayar da abinci. Ta kan lura da yadda iyayenta ke karbar mutane daga kabilu daban daban, musamman cikin karamci. A nan Duan ta gane cewa, musayar al’adu na da ma’ana da taimakawa wajen kyautata fahimtar juna.

Duan ta yi ammana cewa, fasahohin hannu wani nau’i ne na musayar al’adu. “A dakina na nune-nune, mutane na iya jin dadin yadda ake aiwatar da fasahohin hannu na gargajiya na kasar Sin, inda kuma suke samu sabuwar fahimta ko kyautata fahimtarsu game da al’adun kasar Sin. Dakin yana samar da wata dama gare su ta fahimtar karin abubuwa game da kasar sin da al’adun gargajiya na kabilun kasar,” cewar Duan. 

Mutane za su iya gane kyawun fasahohi ba tare da an bayyana shi cikin kalamai ba. Saka mai inganci da launuka masu ban sha’awa da salo masu kyan gani, fasahohin hannu na kasar Sin na kunshe da wani salon kyau na musamman na gargajiya na kasar.

Duan ta ce bangaren sana’arta dake sanya ta farin ciki shi ne, hada mutane masu bambancin launin fata da harsuna da al’adu. Su kan bi yadda Duan ke yin rini da sauran ayyuka, haka kuma sun gano sirri da ruhin fasahohin gargajiya da irin darajar da suke da ita.

Idan suna aikin rini, ‘yan kabilar Bai kan kirkiro salon dake bayyana kyau da fatan alheri da adana tarihinsu.

“Galibin mutane na iya yin watsi da alamomin al’adu, su mayar da hankali kan dabarun fasahohin hannu,” cewar Duan, tana mai cewa, da farko ta kan yi bayani game da alakar salon dake kan aiki da al’adu, kafin daga bisani ta yi bayani kan dabarun rini. 

A lokacin da take koyar da rini, Duan kan yi bayanin yadda za a yi siffar malam-bude-littafi, sannan ta gabatar da alakarsa da al’adun kasar Sin. “A galibin lokuta, Malam-bude-littafi kan alamta soyayya a al’adar kasar Sin. Misali, Masoyan Malam-bude-littafi, wani labarin soyayya ne na gargajiya, daga Sinawa mutanen da. Akwai wurin da ake samun Malam-bude-littafi da ake kira Butterfly Spring, sanannen wuri ne sosai a garinmu. Iyayena sun gaya min cewa, matasa kan je wurin su rera waka idan sun ga wanda suke so,” Duan ke nan yayin da take yi wa dalibanta bayani.

Duan ta tsara wasu darussa bisa mabambantan al’adun gargajiya na kasar Sin, kamar darasin yanka takarda da almakashi a lokacin bikin bazara, da darasin hada fitilun bikin tsakiyar kaka. 

Duan kan yi amfani da wadannan kayayyakin fasahohi domin taimaka mata bayyana ra’ayin rayuwa na al’ummar Sinawa ga mutanen da su shiga ajujuwan. “Ba wai ina son dukkan dalibaina su kware kan al’adun kasar Sin ba ne. Kawai ina son bude musu wata kofa ta yadda za su fahimci kasar Sin da kuma yankin gabashin duniya, domin su yi sha’awar al’adunmu. Abun da nake son yi ke nan”, cewar Duan. 

Ta kan kuma sayar da kayayyaki daban-daban da ‘yan kananan kabilu suka samar, kamar kayayyakin rini da na surfani da tufafi da jakunkuna da sauran wasu kayayyaki a shafinta na yanar gizo. Galibin kayayyakin, mutane masu fasahohin hannu na kananan kabilu a yankin Dali ne suka samar da su.

Ta hanyar sayar da kayayyakin, Duan na fatan taimakawa mutane a fadin duniya fahimtar daraja da muhimmancin fasahohin kabilu daban-daban, wadanda daga bisani, za su taimaka wajen kirkiro wata alaka tsakanin al’adu daban daban.

Duan na kuma fatan kai dalibanta yankin Dali domin musayar al’adu tsakaninsu da magada al’adun kasar Sin da ba na kayayyaki ba. Haka kuma, tana shirin gayyatar kwararrun masana fasahohin gargajiya su gabatar da lakcoci a Birtaniya. “Ina son in kara yada labaran kasar Sin masu kayatarwa ga duniya,” cewar Duan. (Kande Gao)