logo

HAUSA

Gwamnatin Sin ta yanke shawarar baiwa Libya tallafin jin kai na gaggawa

2023-09-18 21:38:12 CMG HAUSA

Hukumar samar da ci gaba da hadin kan kasa da kasa ta kasar Sin, ta bayyana a yau Litinin cewa, gwamnatin Sin ta yanke shawarar baiwa kasar libya tallafin jin kai da ya kai Yuan miliyan 30 (kwatankwacin dalar Amurka miliyan 4.11) cikin gaggawa, don taimakawa kasar wajen tinkarar bala’in mahaukaciyar guguwa, da ambaliyar ruwa, da gudanar da aikin ceto. (Amina Xu)