logo

HAUSA

Tumaki sun taimakawa wajen kyautata lafiyar tunanin dan Adam

2023-09-18 09:56:28 CMG Hausa

 

In an tabo maganar zaman rayuwar yankunan karkara, to, watakila wasu kan tuna da yadda tumaki suke cin ciyayi a tudu. Masu karatu, ko kun san cewa, yin mu’amala da wadannan dabbobin kiwo masu kyau, yana taimakawa wajen kyautata tunanin dan Adam.

Masu nazari daga jami’ar California ta kasar Amurka sun samu sakamakon bincike ba zato.

Jaridar Daily Mail ta kasar Birtaniya ta ruwaito cewa, masu nazarin daga jami’ar California sun fara kiwon awaki 25, masu nau’o’i 4 a jami’ar tun daga shekarar 2021, a yunkurin gano batun cin ciyayi. Ana kiwon wadannan awaki ne a wani wuri na musamman, inda suke cin ciyayi a fili da rana, kuma su koma garkensu da dare. Bayan shekaru 2, masu nazarin sun yi mamaki sosai kan sakamakon nazarinsu, wato baya ga cin ciyayi, samar da taki, da kyautata muhallin halittu, wadannan awaki sun kuma taimaka wa dalibai wajen sassauta matsin lambar da suke fuskanta.

Masu nazarin sun yi karin bayani da cewa, bayan da suka yi bincike kan malamai da dalilai kusan dari 2, sun gano cewa, malamai da dalibai wadanda su kan wuce ta wurin kiwon awakin, ko kuma sukan yi karatu a kusa da awakin, matsin lambar da suke fuskanta ta yi kasa sosai da wadanda ba su taba ganin wadannan awaki ba.

Masu nazarin sun ci gaba da cewa, da farko sun gudanar da nazarinsu ne kan batun cin ciyayi, amma a karshe sun kammala nazari kan yadda awaki suke kwantar da hankulan mutane.

Sun kara da cewa, mutane masu yawa su kan ji farin ciki sosai, duk da cewa hutun da suke yi kadan ne, ta hanyar kallon wadannan awaki ba da wata niyya ba, yayin da suke shan aiki a zaman rayuwar yau da kullum.

Masu nazarin suna ganin cewa, yayin da dalibai masu dimbin yawa suka yi korafin suna fuskantar babban matsin lamba, nazarinsu yana da ma’ana sosai.

Masu karatu, ko a ganinku, yin mu’amala da dabbobin kiwo, yana taimaka muku daidaita matsin lambar da kuke fuskanta, a aiki da ma zaman rayuwa? (Tasallah Yuan)