logo

HAUSA

Za a kammala aikin layin dogo da ya taso daga Kano zuwa garin Maradi a jamhuriyyar Nijar cikin shekara ta 2025

2023-09-18 09:52:50 CMG Hausa

 

Ministan harkokin sufuri a tarayyar Najeriya Sanata Sa’idu Ahmed Alkali ya bayyana gamsuwa bisa yadda aikin layin dogo da ya taso daga Kano a arewacin Najeriya zuwa Maradi dake Jamhuriyyar Nijar ke gudana.

Minista ya bayyana hakan ne a karshen mako a zantawarsa  da manema labarai a garin Dadin-Kowa dake yankin karamar hukumar Kazaure a jihar Jigawa lokacin da yake duba yadda aikin ke gudana. Ya ce, hakika akwai kyawawan alamu dake nuna cewa kamfanin da yake gudanar da kwangilar zai iya cimma wa’adin da aka debar masa nan da 2025.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Aikin wanda zai lankwame tsabar kudi har dala biliyan biyu zai ratsa ta jihar Jigawa ne kafin ya kare a garin Maradi, kuma kamar yadda ministan ya ce, an assasa aikin ne hususan domin bunkasa sha’anin cinikayya a tsakanin Najeriya da Jamhuriyyar Nijar.

Ministan sufurin na tarayyar Najeriya ya ce, ya gamsu sosai bisa irin kayayyakin da aka tanadar domin dai amfani da su wajen shimfida layin dogon.

A lokacin da ministan ya ziyarci jami’ar nazarin harkokin sufuri kuwa dake garin Daura wanda an kirkire ta domin ta samar da kwararrun ma’aikata da za su tafiyar da harkar sufurin jiragen kasan da za su rinka sintiri a kan layin dogon idan an kammala, da ma sauran layikan dogo da ake amfani da su a Najeriya, nan ma ministan ya bayyana gamsuwarsa sosai da nagartar aikin.

“Wajibi ne na yabawa kamfanin gine-gine na kasar Sin CCECC domin jami’ar ta samu ne bisa gudummawarsa domin shi ne yake da kaso 90 na karfin ginin jami’ar. A don haka ya zama lallai na yi kira ga sauran kamfanonin gine-gine da suke aiki a Najeriya da su yi koyi da kamfanin na CCECC wajen samar da wani abu da zai amfani ’yan kasa kamar gina asibitoci da sauran makamantan ayyukan domin kasa ta samu amfana daga ayyukansu.”

A jawabinsa shugaban jami’ar sufurin ta Muhammadu Buhari dake garin Daura, Farfesa Adam Umar ya yi alkawarin cewa, cikin watan Oktoban wannan shekara jami’ar dai za ta fara daukar dalibai.

Ya ce samuwar jami’ar alheri ne babba ba ga Najeriya ba kadai, har ma ga sauran kasashen dake nahiyar Afrika. (Garba Abdullahi Bagwai)NCMEWS