logo

HAUSA

Ci gaban kasashe masu tasowa ya zama dole

2023-09-18 20:00:07 CGTN Hausa

“Yanzu haka kasashe masu tasowa na samun ci gaba cikin sauri, inda suke samar da karin tasiri a duniya. Wannan wani yanayi ne mai yakini wanda ba za a iya sauya shi ba.” Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya fadi haka a kwanan baya, yayin da yake ganawa da takwaransa na kasar Zambia Hakainde Hichilema. Wannan zance ya nuna ra’ayinsa game da sauyawar yanayin da ake samu kan tsare-tsaren duniya.

Hakika ana iya ganin yadda kasashe masu tasowa suke samun karin karfi, bisa tantance wasu abubuwan da suka abku a kwanan baya. Misali, an shigar da kungiyar kasashen Afirka ta AU cikin rukunin kasashe masu karfin tattalin arziki ta G20, kana an yarda da sanya karin wasu mambobi 6 cikin tsarin hadin gwiwa na kasashen BRICS (Brazil, Rasha, India, Sin, da Afirka ta Kudu).

Ban da haka, an gabatar da sabbin matakai na taimakawa kasashen Afirka cimma burinsu na dunkule tattalin arzikinsu waje guda, da zamanantar da kasashensu, wajen wani taron musayar ra’ayi na shugabannin kasashen Afirka da Sin.

Haka kuma, a wajen taron shugabannin rukunin kasashe 77 (wata kungiyar hadin gwiwar kasashe masu tasowa) da kasar Sin, da aka kammala shi jiya Lahadi a kasar Cuba, an gabatar da sanarwar karfafa hadin kan kasashe masu tasowa, da niyyarsu ta kara taka muhimmiyar rawa a harkokin kasa da kasa. Duk wadannan abubuwa sun nuna karuwar karfin kasashe masu tasowa.

Sai dai babu shakka, wannan yanayi mai yakini da kasashe masu tasowa suke ciki zai janyo hassada, da kokarin hana ruwa gudu daga wasu kasashe masu sukuni. Hakan ya sa ake yin kokarin bayyana ra’ayin rashin amincewa da kashin dankali da ake yi a duniya, a wajen taron rukunin kasashe 77 da kasar Sin. Inda dimbin shugabanni, da manyan jami’ai na kasashe masu tasowa suka yi kira da a kawo karshen wani “ tsarin kasa da kasa mai cike da ayyukan kwatar dukiyoyi”, tare da bukatar dukkan kasashe masu tasowa da su gyara ka’idojin da ake bi yayin da ake tafiyar da harkokin kasa da kasa.

Ban da haka, sanarwar Havana da aka gabatar wajen taron ta nuna yadda ake kin yarda da tsare-tsaren duniya maras adalci, inda aka yi Allah wadai da matakan tilastawa sauran kasashe yin wani abu, da sanyawa kasashe masu tasowa takunkumi, da hana su samun damar raya fasahohi na zamani, da dai sauransu.

Dalilin da ya sa kasashe masu tasowa ke kin amincewa da tsoffin tsare-tsaren kasa da kasa, shi ne suna neman maye gurbinsu da wani sabon tsari mai adalci, wanda zai ba su damar kare moriyar kai, da neman samun ci gaban tattalin arziki ba tare da wata matsalar da aka haifar musu ba. Sai dai ta yaya za a iya cimma wannan buri? A wajen taron rukunin kasashe 77 da kasar Sin na wannan karo, bangaren kasar Sin ya ba da shawara cewa, da farko, a yi kokarin dogaro da kai, da magance yin fito-na-fito da sauran kasashe, da neman daidaita sabanin ra’ayi ta hanyar sulhu. Na biyu shi ne, a yi kokarin tabbatar da adalci yayin da ake kula da harkokin kasa da kasa, da kare moriyar kasashe masu tasowa, da sanya su zama masu fada a ji a duniya. Kana abu na uku shi ne, a yi karin hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa, don tabbatar da ci gaban tattalin arzikinsu, da daga matsayinsu a duniya ta fuskar raya sabbin fasahohi da sana’o’i.

Hakika a wannan zamanin da muke ciki, karfin kasashen yamma a fannin tattalin arziki da siyasa na raguwa, don haka sun kara nuna halayyarsu ta son kai, da rashin hankali. Wannan ya sa kasashe masu tasowa ke bukatar yin hadin gwiwa a tsakaninsu, don magance a ci zarafinsu. Daga baya wannan yanayin da ake ciki ya sa muke ganin dimbin kasashe masu tasowa ke kokarin rufa wa juna baya a sassa daban daban, da fito da murya iri daya. Ta la’akari da yadda kasashe masu tasowa ke kunsar mafi yawan kasashe da al’umma a duniyarmu, hadin gwiwar su zai tabbatar da hauhawar matsayinsu a duniya a kai a kai. (Bello Wang)