logo

HAUSA

Fada ya rincabe a birnin Khartoum tsakanin dakarun Sudan da ba sa ga maciji da juna

2023-09-17 15:36:08 CGTN Hausa

Fada ya kara rincabewa a birnin Khartoum, tsakanin dakarun gwamnatin Sudan ko SAF, da rundunar sojojin ko ta kwana ta RSF, a gabar da rikicin kasar ke shiga wata na 6.

Rahotanni na cewa, dakarun sassan biyu sun yi ta dauki ba dadi a sassan Khartoum tun daga jiya Asabar. An ce dakarun RSF sun rika harba makamai kan helkwatar babbar sansanin SAF dake tsakiyar birnin Khartoum, da ma wasu sansanonin sojin gwamnati dake daura da biranan Omdurman da Bahri.

Wasu majiyoyin soji sun ce dakarun na gwamnati ko SAF, sun rika tare hare haren sojojin RSF, daga manyan sansanonin su na arewa maso gabas, da kudu maso yamma, yayin da sojojin gwamnatin na SAF suka yiwa abokan fadan su na RSF mummanar barna ta rayuka da makamai.

A birnin Bahri wanda ke arewacin Khartoum, shaidun gani da ido sun ce dakarun RSF, sun rika harbi da manyan bindigogin atilari, kan cibiyar na’urorin sadarwa na sojojin gwamnati.

Yayin da wannan dauki ba dadi ke shiga wata na 6, dakarun RSF na ci gaba da rike ikon kaso mafi girma na birnin Khartoum, da ma wasu yamkunan yammacin kasar, yayin da sojojin gwamnati na SAF, ke rike da akasarin yankunan arewaci da gabashi da tsakiyar kasar ta Sudan. (Saminu Alhassan)