logo

HAUSA

Hukumar tsaro ta Civil Depence ta sha alwashin kare makarantu da malamai a jihar Borno

2023-09-17 14:56:14 CMG Hausa

Hukumar tsaron farin kaya ta Civil Depence a tarayyar Najeriya ta sha alwashin kara kaimi wajen kare makarantu da malamai a jihar Borno daga fuskantar hare-haren ’yan kungiyar Boko Haram.

Babban kwamandan hukumar Dr. Ahmed Abubakar Audi ne ya bayyana hakan bayan kammala shirin bayan da horo na tsawon kwanaki biyu da aka shiryawa jami’an hukumar dake jihar Borno a kan sabbin dabarun tsare makarantu daga farmakin ’yan ta’adda.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Dr. Ahmed Audi ya ce, hukumar ta samar da dakarun musamman da za su iya bayar da kulawar da ta kamata ga dalibai da malaman dake daukacin makarantun shiyyar arewa masu gabashin Najeriya. 

Shugaban hukumar ta Civil Depence wanda ya samu wakilcin mataimakin kwamanda-janaral na hukumar Waziri Babo Goni ya ce, a baya daliban makarantun dake jihohin Yobe da Borno sun fuskanci barazanar ta’addanci daga ’yan kungiyar Boko Haram, inda a shekara ta 2014 ’yan kungiyar suka sace sama da mata 200 daga makarantar sakandiren Chibok, duk dai a wannan lokaci kuma ’yan ta’addan kungiyar ta Boko Haram suka yanka wasu dalibai a makarantar gwamnatin tarayyar dake Buni Yadi.

“Hukumar ta samar da wani sabon tsarin bada agajin gaggawa ga duk wani dake fuskantar barazanar tsaro.” 

Inda ya ce, akwai dakarun musamman da aka baiwa horo don ba da agajin gaggawa kuma wannan ce ta sanya ma aka gudanar da irin wannan shiri na ba da horo a birnin Maiduguri da nufin kare dalibai daga ta’addancin kungiyar ta Boko Haram, inda ya yi kira ga wadanda suka halarci wajen wannan shiri na ba da horo da su yi amfani da ilimin da suka samu wajen tattara bayanan sirri da kuma yin bincike da nufin dakile hare-haren ta’addanci a wuraren da suke aiki. (Garba Abdullahi Bagwai)