logo

HAUSA

Motoci biyu ne aka kame makare da tabar wiwi da alburusai da ake kokarin shigowa da su Najeriya daga Ghana

2023-09-16 16:13:03 CMG Hausa

Rundunar ‘yan sanda a jihar Kebbi dake arewacin Najeriya ta sanar da kame wasu manyan motoci biyu makare da kunshin tabar wiwi da kuma alburusai da ake kokarin shigowa da su Najeriya daga kasashen Ghana da jamhuriyar Benin.

A lokacin da yake gabatar da motocin ga ‘yan jaridu a hedkwatar ‘yan sanda dake birnin Kebbi, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar SP Nafi’u Abubakar ya ce a karshen makon jiya ne jami’an sintiri na rundunar suka samu nasarar kame motocin a yankin karamar hukumar Bagudo.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

 

SP Nafi’u Abubakar ya ce tun bayan kame motocin ne aka fara gudana da bincike a kan motocin da direbobi motocin da kuma masu kayan, inda bayan kammala binciken aka gano daga inda kayan suke da kuma nau’in abubuwan da suke kunshe cikin kwantainonin motocin biyu.

An dai kiyasta kudin kayan kan tsabar kudi kusan sama da naira miliyan dari 6.

“Jami’an mu wato boda fatrol da aka ajiye a garin Saran-Fomaje dake cikin gundumar Tsamiya a karakshin karamar hukumar Bagudo sun samu nasarar kama wata mota da ta taso daga kasar Ghana ta biyo ta jamhuriyar Benin tana kan hanyar zuwa Legos, bayan gudanar da bincike sun samu kulli na tabar wiwi kimanin 4,927.”

SP Nafi’u Abubakar haka kuma ya shaidawa manema labaran cewa, a mota ta biyu kuma da jami’an nasu suka kama sun gano wasu haramtattun kayayyakin.

“Ita ma tana dauke da alburushi kimanin 7,500, haka a cikin wannan mota jami’ai namu sun samu nasarar kame wani ganye da ake tunanin tabar wiwi ne guda 4,906 wanda duka in ka hada, kudin kayayyakin motocin biyu ya fi karfi naira milyan 600.”

Kakakin rundunar ‘yan sandan ta jihar Kebbi ya jaddada kudirin cewa, “rundunar ‘yan sanda ta jihar Kebbi ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin ta yaki laifuka da masu aikata laifuka a wannan jiha har sai mun samu ingantaccen kwanciyar hankali, haka zan yi amfani da wannan dama in yi kira ga al’umma da su cigaba da baiwa jami’an ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro hadin kai, idan sun ga wani abu su yi kokari su sanar da mu cikin lokaci don mu dauki mataki cikin gaggawa.”(Garba Abdullahi Bagwai)