logo

HAUSA

Ina Ne Damar Kasuwa Ta Gaba? Sun Ce Har Yanzu Tana A Sin

2023-09-16 16:46:26 CMG Hausa

Alkaluman kididdigar tattalin arzikin kasar Sin da aka fitar a jiya Jumma’a, na nuna cewa, yawan hajoji da kayayyakin masarufi da Sin ta sayar, ya karu da kashi 4.6 cikin 100 kan na shekarar bara, wanda ya karu da kaso 2.1 cikin 100, fiye da na watan da ya gabata. "Alkalumann tattalin arzikin kasar Sin sun inganta", "Cinikayyar hajojin kasar ta zarce yadda ake zato". Kafofin watsa labaru na kasashen waje sun mai da hankali kan farfadowar tattalin arzikin kasar Sin.

Baya ga wadannan alkaluma, akwai kuma damarmaki na yin kasuwanci da baki daga waje ke sha'awa matuka. Tun daga farkon wannan shekara, farfadowar tattalin arzikin duniya yake fuskantar tafiyar hawainiya, kuma sakamakon durkushewar manufofi a manyan kasashe masu karfin tattalin arziki ya fito fili. Tattalin arzikin kasar Sin ya jure matsin lamba, ya kuma ci gaba da farfadowa, kuma yana ci gaba da zama muhimmin injin na ci gaban tattalin arzikin duniya.

Ga masana'antun kasa da kasa kuwa, kyakkyawan fata abu ne mai muhimmanci matuka lokacin da kasuwar duniya ke fama da rashin tabbas. A bana ana hasashen bunkasar tattalin arzikin kasar Sin za ta kai kusan kashi 5 cikin 100. Bankin duniya, OECD da Asusun ba da lamuni na duniya IMF, duk sun yi hasashen cewa, tattalin arzikin kasar Sin zai bunkasa da kashi 5.6, da kashi 5.4 da kuma kashi 5.2 cikin 100 bi da bi a shekarar 2023.

A sa'i daya kuma, ta fuskar manufofi, sabanin wasu kasashen yammacin duniya, wadanda sau da dama suke sauya ra’ayi, kwanciyar hankali da dorewar manufofin tattalin arzikin kasar Sin, sun karfafa gwiwar kamfanonin kasa da kasa. Fito da tsarin tarukan tattaunawa, wanda ya hada da na kamfanoni masu jarin waje, zai taimaka wajen magance matsalolin da kamfanoni ke fuskanta a kan lokaci da kuma saukaka ci gaban su. McKinsey ya yi imanin cewa, kasar Sin na daya daga cikin manyan kasashe a duniya da ke samar da muhimmiyar damammakin ci gaba ga kamfanonin kasa da kasa.(Ibrahim)