logo

HAUSA

MDD ta kaddamar da neman tallafi ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Libya

2023-09-15 11:12:16 CMG Hausa

A Jiya Alhamis ne masu aikin jin kai da abokan hulda na MDD suka kaddamar da neman tallafi na dalar Amurka 71.4 don biyan bukatun gaggawa na ’yan Libya da ke fama da bala’in ambaliyar ruwa.

Kudaden za a tallafawa mutane 250,000 ne daga cikin mutane 884,000 da aka kiyasta za su kasance mabukata nan da watanni uku masu zuwa, a cewar ofishin kula da ayyukan jin kai na MDD (OCHA). Ana iya sabunta neman tallafin da zarar an samu karin bayanai.

Yankunan da ibtila’in ya fi shafa sun hada da Derna, Albayda, Soussa, Al-Marj, Shahat, Taknis, Battah, Tolmeita, Bersis, Tokra, da Al-Abyar, a cewar OCHA. ’Yan gudun hijirar sun nemi mafaka a makarantu da otal-otal.

Masu aikin jin kai sun ba da rahoton cewa, asibitin Albayda da ke kula da yankin Jabel Akhdar baki daya ya cika da ambaliyar ruwa, lamarin da ya tilasta kwashe majinyatan sashen kula da marasa lafiya zuwa asibitoci masu zaman kansu tare da mayar da sauran majinyata wasu wurare.

Mataimakin sakatare janar na MDD mai kula da ayyukan jin kai Martin Griffiths, ya ce girman bala'in ambaliyar yana da ban tsoro, inda ta shafe wasu unguwanni da iyalai baki daya daga taswira, ba zato ba tsammani ambaliyar ta tafi da su. (Yahaya)