NSA Ta Yiwa Jami’ar NPU Kutse Ta Yanar Gizo
2023-09-15 19:42:15 CMG Hausa
Kwanan baya, an samu babban ci gaba wajen bin bahasin batun kutsen da aka yiwa jami’ar masana’antu ta Arewa maso yammacin kasar Sin wato Northwestern Polytechnical University NPU a Turance ta yanar gizo, inda kasar Sin ta yi nazari kan wata manhaja, tare da tabbatar da yadda ma’aikatan hukumar kula da tsaron kasar Amurka wato NSA ke da hannu cikin batun. Lamarin ya kasance a matsayin wata shaida da ke nuna cewa, gwamnatin Amurka ta yiwa wasu kasashe kutse ta yanar gizo.
A daidai wannan lokaci, ma’aikatar tsaron Amurka ta kaddamar da takaitaccen bayani kan manyan tsare-tsaren yanar gizo na shekarar 2023, inda ta sake baza kalaman “kasar Sin na haifar da barazana”. Yayin da Amurka take satar bayanan sirrin kasar Sin ta hanyar manhajar musamman, ta kuma dora wa kasar Sin laifin, abin da take yi ya nuna cewa, tana mayar da kasar Sin a matsayin babbar abokiyar takararta. Bugu da kari, yayin da karfin shugabancin 'yan siyasar Amurka ya ragu, suna kokarin baza kalaman “wasu na haifar da barazana” don karkatar da hankulan mutane. A sa'i daya kuma, hakan ya baiwa Amurka wani uzuri na cin zarafin kasar Sin ta fuskar yanar gizo da masana’antun sadarwa, wanda hakan ya share mata hanya ta kara yin kutsen yanar gizo a kasashen waje.
Yadda aka samu babban ci gaba wajen bin bahasin batun yi wa jami’ar NPU kutsen ta yanar gizo, ya nuna cewa, kasar Sin na da karfin kare kanta daga kutsen yanar gizo daga ketare, tana kuma da aniyar kiyaye tsaron yanar gizo a duniya. An yi imanin cewa, sakamakon kyautatuwar kwarewar kasashen duniya ta fuskar tsaron kansu a yanar gizo, ya sa za a sa aya kan yadda Amurka take yin danniya a yanar gizo. (Tasallah Yuan)